Mai Gabatarwa: Dr. Salihu Lukman
TATTAUNAWA 001 (Rana: 18.11.19)
Abubuwan da suka biyo bayan tattaunawar dandalin ciwon sukari (Diabetic Monitoring Forum 1 – DMF1) wanda na gudanar akan taken, “Shinkafa – Mai kyau da mara kyau”.
1. Brown rice (shinkafa mai launin ruwan kasa) tafi gina jiki saboda ita ba’a surfeta ba. Masu ciwon sukari ya kamata su guji farin shinkafa (shinkafan tuwo da na wara). Duk lokacin da zaku ci shinkafa mara launin ruwan kasa, yi amfani da shawarar girke-girken na shinkafa a karshin lamba (2) da ke ƙasa kuma ku kula da yawan abincin.
2. Yanda ya kamata a hada shinkafa da wake:
(a) Yi amfani da 30 % (shinkafa): 70 % (wake). Kuna iya ƙara alayyaho ko wasu kayan lambu.
(b) Yi amfani da 30% (wake): 70% (shinkafa). Wannan dole ne ya kasance tare da miyan alayyaho ko kuma sauran kayan lambu ko kuma a sa salatin (salad).
3. Salad: Guji yin amfani da kirim na salatin domin yana dauke da sukari, mai (wanda ake ba a so) mai yawa kuma yana da wadatar kalori. Yawanci mafi kyawun kayan adon salatin sune waɗanda suke tushen-mai saboda waɗannan nau’ukan sutturar an yi su ne da mai mai kawo lafiyar zuciya kamar man zaitun, man kuli-kuli, da sauransu ko vinegar. Ina bayar da shawarar yin anfami da apple cider vinegar saboda yana taimakawa wajen rage sukarin jini kuma yana taimakawa wajen rage kiba.
Ka na iya haɗa salatin ka da wadannan: tumatir, tattasai, karas, kokwamba, albasa, kabeji, letas, barkono kore, albasa da sauransu.
Ka kula: Ya kamata ka dinga gwada sukarin jinin ka duk lokacin da ka canza abincin ka daga mai karancin abin gina jiki zuwa mai gina jiki idan ka kasance kana amfani da maganin ciwon sukari don gujewa karancin sikari a jinin ka.
4. Farin sukari, mai launin ruwan kasa (ciki har da mazarƙwaila) wato brown sugar, raw sugar: Dukkansu basu da banbanci iri daya ne wajen yanda suke aiki a jikin mai ciwon sukari.
TATTAUNAWA 002 (Rana: 21.11.19) Part 1
Ciwon sukari (DMF1 & DMF2)
Mai Gabatarwa: Dr. Salihu Lukman
Taken Darasi: Taliya da dangin ta: Mai gina jiki da kuma mara gina jiki
TALIYA, MACARONI, CUSCUS
Wadannan nau’ukan abincin suna zarkame da sukari wato carbohydrates, kuma idan ana cin su da yawa za su iya kawo kiba, da kara kumburin ciwo, sannan suna daga sukarin jini. Sabili da haka, ya kamata a kaurace musu gabaki daya. An yi su ne daga faran alkama wato wanda aka surfeta.
Idan mutum ya kasance dole sai ya ci su, to ya kamata ya ci su tare da kayan lambu da yawa ko kuma salatin (salad) domin su kara ma wadannan abincin sinadarin gina jiki kuma su rage yanda sukarin jinin mutum zai karu da sauri.
HANYOYIN DA ZA A IYA KAUCE MA ILLOLIN TALIYA DA DANGIN TA
- A nemi taliya ko macaronin da aka yi su daga alkaman da ba a surfe ba wato whole-wheat.
- A nemi taliyan da aka kara mata abubuwan gina jiki kaman su farin cikin kwai (egg whites), legumes (dangin wake), da sha’ir (barley) da kuma oats (hatsi).
- Ko kuma a nemi taliyan da akayi da chickpeas ko brown rice (shinkafa mai launi ruwan kasa), ko tamba.
TATTAUNAWA 002 (Rana: 21.11.19) Part 2
Mai Gabatarwa: Dr. Salihu Lukman
Taken Darasi: INDOMIE KO KUMA INSTANT NOODLES: Mai gina jiki da kuma mara gina jiki
Instant noodles (wato dangin su Indomie da sauran su) su ne irin taliyan da aka riga aka girka su tun kafin a siyar da su fakiti-fakiti ko kofi ko kuma tasa.
Abubuwan da ake yin wadannan taliyan sun hada da filawa, gishiri da manja. Kuma suna dauke da gishiri mai yawa, magi, da kuma sinadarin nan mai suna monosodium glutamate (MSG).
Bayan an kammala yin irin wadannan taliyan a kamfani, ana turara su, a busar da su sannan a saka su a fakiti-fakiti domin siyar wa.
Kalori (calorie) da fiber (wato kaman dussa kenan wanda jikin dan’adam baya iya amfani da shi amma kuma yana taimakawa wajen rage saurin tashin sukarin jinni) da kuma saukan shi) da furotin (protein) suna da karanci a yawancin irin wadannan taliya, sai dai kuma suna da yawan kitse (fat), da sukari (carbs) da sodiyom (sodium) da kuma wasu daga cikin bitamin (vitamins) da ma’adinai (minerals) wadanda jiki ke bukata.
Dole mai ciwon sukari ya guje ma irin wadannan taliyan, amma idan ya zama babu makawa sai an ci su, to ya kamata jibga musu kayan lambu (kaman su alayyaho, karas, kukumba, latas, da dai sauran su) domin su kara musu abubuwan gina jiki. Sannan kuma bayan haka, ayi amfani da kadan ne kada a cika shi taliyan.
Idan mutum zai iya samun Instant Noodles din da basu da sodiyom (sodium) da yawa, kuma an yi su ne daga hatsin da ba a surfe ba wato whole-grain, to irin wadannan sun fi kara lafiya. Duk da haka, su din ma, ya kamata a kara musu kayan lambu da kamar wake ko nama (wato protein).
Hattara: Mai ciwon sukari ya dunga awon sukarin jinin sa duk sanda ya chanza irin abin da saba ci matukar yana shan maganin ciwon saboda guje ma yanayin rashin sukari kuma wato hypoglycemia.
TATTAUNAWA 006 (Rana: Laraba, 04.12.19)
Mai Gabatarwa: Dr. Salihu Lukman
Taken Darasi: Yanda mukayi taimakekeniya wajen yada muguwar cutan nan mai suna CIWON SUKARI (Diabetes) da kuma yanda za mu iya shawo kan ta a cikin kwana 7 kacal.
Wuri: Ciwon sukari, WhatsApp (DMF3) & Telegram (DMF4) Groups
Lokaci: 7 – 8 pm, Lokacin Najeriya
Katin gayyatar shiga dandalin mu na Telegram: https://t.me/ciwonsuga2
Sai kun zo domin tattaunawa a kan yanda za a iya sarrafa sukarin jini ya kasance bai hau sama ba kuma bai sauka kasa ba. Ku shirya tambayoyin ku ko sharhi wanda za ku gabatar bayan na kamala na wa gabatarwan.
TATTAUNAWA 006 (Rana: Laraba, 04.12.19)
Mai Gabatarwa: Dr. Salihu Lukman
Taken Darasi: Yanda mukayi taimakekeniya wajen yada muguwar cutan nan mai suna CIWON SUKARI (Diabetes) da kuma yanda za mu iya shawo kan ta a cikin kwana 7 kacal.
Mun taimaka da yaduwar cututtukan sukari ta hanyoyi 2:
- a) Yanayin abincin mu
- b) Salon rayuwa wanda babu kazar-kazar
Yadda mu ka canza daga zaɓuɓɓukan abinci na gari mafi ƙoshin lafiya zuwa ga abinci mai haifar da rashin lafiyar masu ciwon sukari.
Kodayake, ni dan saurayi ne (wataƙila ba zan kai shekara 25 ba 🤔🤫😜), zan ba ku jerin lokutan wannan mummunan canjin, daga mai kyau zuwa mara kyau zuwa mafi muni.
1980s – Farkon 90s: Shahararrun girke-girke a cikin yankinmu (Zaria, Nigeria)
- Faten surfaffen masara (duk da yake daga baya an koma yi da shinkafa), doya ko wake tare da alayyaho, rama ko yakuwa sannan ya ji sauran kayan girki. [Mai gina jiki ne, sannan ya na da fiber sosai, ba a cika yin irin wannan abincin ba a yanzu]
- Dambu: Mai gina jiki ne, sannan ya na da fiber sosai, ba a cika yin irin wannan abincin ba a yanzu
- Tuwon kasambara wanda ake yi da masara niƙaƙƙe amma ƙura-ƙura. [Mai gina jiki ne idan an yi shi da masaran da ba a surfe ba, ba a yin irin wannan abincin a yanzu]
- Tuwon surfaffen masara ko dawa. [Mai gina jiki ne idan an yi shi da hatsin da ba a surfe ba. A yanzu tuwon faran shinkafa da semovita su ne aka fi yi. Amma za a iya amfani da acca, tamba, oats, alkaman da ba a surfe ba a madadin tuwon farar shinkafa da semovita saboda karin lafiya]
- Doya da sakwara. Ba mai gina jiki ba ne amma za a iya kara mai sinadarin gina jiki ta hanyar yin faten sa tare da wake da kayan lambu sosai amma doyan kadan.
- Farar shinkafa ko ta wara. Ita wannan ba a cika cin ta ba sai dai ma su kudi, an fi yin amfani da ita lokutan shagulgulan Sallah da kuma sauran bukukuwa kaman daurin aure da suna. [Ba mai gina jiki ba ne amma za a iya kara mai sinadarin gina jiki ta hanyar girka shi tare da wake da kayan lambu mai yawa. Yanzu ta mamaye duk gidaje, talakawa ne ko kuwa mai kudi]
- Taliyan da akeyi da injin hannu. Ba mai gina jiki ba ne amma za a iya kara mai sinadarin gina jiki ta hanyar girka shi tare da wake da kayan lambu mai yawa. A yanzu ba a yi da injin hannu din, amma wadanda ake saka su a leda wato wanda ake shigowa da su daga ƙetare sun mamaye ko ina. Yanzu sun mamaye duk gidajen talakawa da masu kudi.
- Dan wake. Mai gina jiki ne amma idan an yi amfani da niƙaƙƙen wake ko tamba ko oats. Ba mai gina jiki ba ne idan an yi amfani filawan da aka samo daga surfaffen alkama ammaza a iya kara mai sinadarin gina jiki ta hanyar kara mai kayan lambu mai yawa irin su kukumba da tumatir. Ba a cika yin dan wake ba yanzu.
- Mai gina jiki ne idan an yi shi da waken da ba a chire bayan shi ba. Za a iya kara inganta shi idan aka chi shi da miyan alayyaho. Har yanzu ana yin irin wannan abincin]
- Fura da nono. Ya na gina jiki idan ba a sa sukari ba kuma ba a surfe geron ba. Za kuma a iya yin furan da acca ko tamba. Har yanzu ana yin irin wannan abincin.
- Ƙwadon zogala, rama ko yakuwa. Suna gina jiki sosai amma ba a cika girka su ba yanzu.
- Dankalin Hausa da ƙuli-ƙuli. Duk da yake ya fi dankalin turawa gina jiki amma ya kamata mai ciwon sukari ya yi nesa da shi.
- Koko da kunu. Masu gina jiki ne amma idan an yi amfani da hatsin da ba a surfe ba. Za a iya yin amfani da acca, tamba, oats ko kuma alkaman da ba a surfe ba. Har yanzu ana shan su tun ba ma da azumi ba.
A halin yanzu, mun watsar da duk kyawawan abubuwan da muka ambata a sama na wadanda suka danganci abincin gina jiki. Mafi muni kuma, mun maye gurbinsu da wadanda basa gina jiki sai ma dai haddasa mana cututtuka suke yi.
A zamanin yau, shinkafa, taliya da Indomie sun mamaye kowane gida ba tare da la’akari da kabila ko yanki ba.
Wadannan abincin sune wasu manyan dalilan da yasa cutar siga ta kama mutane a cikin kowane gida kuma yadda yake kama mutane yana ƙaruwa kamar wutan daji.
b) Salon rayuwa wanda babu kazar-kazar wato zama wuri daya a jima ba tare da motsa jiki ba.
1980s – Farkon 90s (Zaria, Nigeria):
Ana tafiya mai nisa, babu dan acaba/Okada/going (mai jigilar babur), kekuna da yawa, akwai matuƙar ƙarancin babura da motoci, manoma da yawa, masu surfen hatsi ta hanyar amfani da turmi da taɓarya suna da yawa.
Daga tsakiyan 90s – Yanzu (Zariya, Nigeria): Babu sauran yin tafiya mai nisa da ƙafa, kasancewar Okada (mahaya babur)/acaba da kuma Keke NAPEP a cikin kowane tsayayyiyar hanya a kusan dukkanin garuruwa ban da garuruwan da aka hana masu ababen hawan Babura wadanda ƙalilan ne sosai, ƙarancin kekuna, yawancin mutane yanzu suna da motoci, an sayar da gonaki da dama, manoma sun yi ƙaranci, babu masu yin surfen turmi da tabarya saboda injin gyaran hatsi yam aye gurbin su.
Menene tasirin waɗannan canje canjen da muka zayyana a sama game da abincin mu da kuma salon rayuwar mu na rashin kazar-kazar?
Rayuwa mai taɓarɓarewa irin na zama wuri daya wanda ke haifar da karuwar yawan kiba, hauhawar jini, masu ciwon sukari, matsalolin zuciya, da sauransu.
Yanzu, ta yaya za mu iya dakatar da wannan MAYE da ake kira da ciwon sukari (type 2) daga cinye mu ko masoyanmu?
Wannan ita ce tambaya mai girma, amma kuma ga ta da amsa mai matuƙar sauƙi.
Tunda mun rigaya mun gano musabbabin matsalar mu wadanda suke jawo ciwon sukari, to, dole ne mu koma da baya da baya kamar haka.
Dole ne mu nisanci DUKKANIN ABINCIN DA BAYA GINA JIKI SOSAI. Ta yaya?
(a) Kada a taɓa amfani da surfaffen hatsi kamar gero, masara, dawa, alkama (idan mun faɗaɗa, da duk wani abin da akayi da farin filawa kamar semovita, taliya, macaroni, Indomie, farin burodi, kek, meatpie, donot, chin chin, da sauransu).
(b) Guje ma farar shinkafa ko kuma na wara gaba daya. Yin amfani da shinkafa launin ruwan kasa kawai.
(c) Tsanan ta amfani da oats, tamba, acca, alkaman da ba a surfe ba don tuwo, koko, kunu, fate, dan wake, kek, fura da sauransu.
(d) Guje ma yin amfani da sukari ko kowane kayan zaki irin su abubuwan sha, ruwan ‘ya’yan itace, biski, da sauransu.
(e) Tsananta amfani kayan lambu da salad a cikin abincin mu.
(f) Tsananta shan ‘yan’yan itace da kayan marmari da ganyayyaki (musamman ma karas, apples, gyada da aka dafa, ayaba, inabi, bawi, avocado, da dai sauransu) na kowane nau’in kuma a kowane lokaci banda abarba (tana iya daga sukarin jini da yawa).
(g) Guje ma yin amfani da sukarin da ake kira na mai ciwon sukari (sweeteners) ko lemun kwalba (Coke) wanda babu sukari a ciki gaba ɗaya.
(h) Guje ma man naman dabbobi gaba daya, da kuma rungumar man zaitun (don dafa abinci, da sauransu) ko kuma tsarkakakken mai wanda dillalan kuli-kuli suke siyarwa. Rage cin naman manyan dabbobi (saniya, rago, raƙumi), ƙara himma wajen cin farin nama (kamar kifaye masu maiƙo sosai). Guje ma margarine, Blue Bland, man shanu sai a maye gurbin su da tunkuza.
(i) Kada a jinkirta yin karin kumallo da abincin da ya ƙunshi sitaci (starch) kadan, furotin mai yawa da mai mai yawa sannan ku guji bari sai kun ji yunwa sannan za ku ci abincin a koda yaushe matuƙar ba lokacin azumi ba ne. A lokaci guda kuma, a tabbatar da cewa an rage yawan abincin da za a ci a lokaci guda, saboda zaku iya samun hyperglycemia ko da kuwa kuna cin da abinci mai gina jiki ne amma da yawa. Zaku iya yin nazarin jadawalin ire-iren abincin na a ƙasa don ku inganta na ku.
(j) Mallakar na’uran gwada sukarin jinni wato glucometer tare da yin gwajin akai-akai har sai an sami kwanciyar hankali a matakin sukarin jinin mai ciwon.
(k) Guje ma rayuwan da ba bu motsa jini gaba daya. Za a iya yin tafiya na mintina 30 zuwa awa 1 a kowace rana (aƙalla sau 5 a mako) bayan tuntuɓar likitan ka kuma ka guji zama a wuri guda fiye da awa 1 ba tare da motsawa ba kamar na minti 5 a kowace awa. Misali, hawa gidan bene ta matakala, yi la’akari da samun teburin yin aiki a tsaye ko teburin da ake dorawa akan treadmill (wato mashin motsa jiki na cikin gida), yin ayyukan gida da kan ka, mimmiƙewa lokacin da mutuum yake kallon talabijin idan sun tafi hutun yin tallace-tallace, samun lambun da za ka dunga kulawa da ita, tafiya mafi tsayi a filin ajiye motoci (wato mutum ya dunga ajiye motar sa a wajen da sai ya yi tafiya ma dan tsawo kafin ya isa inda za shi), musanya motar da keke, gwada yin amfani da manhaja ko na’uran kiyaye motsa jiki, da dai sauransu.
(l) Guje ma shan taban sigari da barasa.
Ina mai tabbatar mu ku cewa idan har za ku iya kiyaye waɗannan abubuwan (a – l), ba sukarin jinin ku ne kawai koma dai dai ba, zai kasance kun yi rigakafin hauhawar jini da cututtukan zuciya gaba daya.
DUTSE 1 YA KABO TSINTSAYE 3 KENAN!
Akwai wasu ganyayyaki da, kayan ƙanshi, ko tsire-tsire wadanda ba su da adadi kuma waɗanda aka tabbatar da cewa suna iya saukar da sukarin jinin mai ciwon sukari a kimiyance kamar su kubewa, kanumfari, zogala, ruwan zam-zam, dabino, zaitun, baure, da sauransu
https://www.sciencedirect.com/science/article/pii/S1658361216000032
Amma fa ba sa yin aiki nan take, kuma babu wani maganin gargajiya ko na baturen da zai iya kawar maka da matsalan sukarin jinin ka nan take. Dole mutum sai lizimci amfani da wadannan tsirrai a koda yaushe kafin ku amfana da tasirin su.
Ina mai ƙalubalantar duk wani mai ciwon sukari a cikin wannan dandalin wanda matakan sukarinsa na jini ya ke zarce ƙima – a yau ya hau (hyperglycemia) a gobe kuma ya sauka can ƙasa (hypoglycemia) – da ya gwada wadannan ƙa’idodin da na bayar a sama (a – l) har na kwanaki 7 kacal ni kuma ina mai tabbatar mishi da cewa matakin sukarin jinin ka ba zai sake yin maka sama da kasa ba.
A taƙaicen taƙaitawa ma kila likitan ka ma sai ya ƙara yin nazarin magungunan ko kuma ya dakatar da kai daga shan su gaba ɗaya ma.
Babu sihiri ko rufa ido a nan. Allah Madaukakin Sarki Ya riga Ya Yi muku tanadin mafitar wannan ƙangi a tafin hannun ku.
Ina da buƙatar waɗanda za su jarabta wannan tafarkin (masu ciwon sukari type 2) – waɗanda matakan sukarin jinin su yake hauhawa da sauka har ya wuce matakin 11.1 mmol / L, 200 mg / dL ko ya sauka ƙasa da 3.9 mmol / L, 70 mg / dL kuma wadanda za su iya bin waɗannan ƙa’idodin (a – l) sau da ƙafa kuma za su iya bibiyan sukarin jinin su akai akai har na tsawon kwanaki 7 kacal.
Bari in ba ku labarin nasarorin da muka samu guda 2 daga masu ciwon sukari waɗanda suka gwada waɗannan ka’idojin.
1 Ni a karan kai na:
Na kasance ina amfani da alluran insulin tare da shan maganin ciwon sukari metformin na tsawon watanni 2 a cikin 2015 bayan da aka gano cewa ina dauke da ciwon sukarin. A watan Yuni na 2016, a lokacin Azumi sai awon sukarin jini na ya ƙi daidaituwa yanda ya kamata, sai ya hau awa biyu bayan na ci sahur, idan na kara yawan shan maganin kuma sai ya sauka can ƙasa (hypoglycemia) kafin in sha ruwa da mangariba.
Wannan mawuyacin yanayin ya sa nima da dauki wani tsatstsauran mataki a game matsalan. Sai kawai na dakatar da shan maganin ciwon sukarin gaba daya na kuma tsayar da azumin, sai na aiwatar da duka ƙa’idodin da na lissafa a baya (a – l), daga nan kuma sai awon sukarin jini na ya daidaita tsaf A CIKIN KWANA DAYA RAK BA MA KWANAKI 7 BA. Tun daga wancan lokacin na kasance ina rayuwa ta a cikin ƙoshin lafiya, ba tare da na sake shan wani magungunan masu ciwon sukari ba ko yin alluran insulin ba. Bugu da ƙari ma, na zaftare ƙiba har kilo 20 kuma har yanzu ina nan ina ƙidaya.
2 Daya daga cikin mambobin mu na musamman (wato waɗanda suka zaɓi cika tambayoyinmu ta yanar gizo [https://forms.gle/PQU9YeyWyWAdzFe79] don samun ra’ayinmu game da yanda ya kamata su bibiyi sukarin jinin su ko kuma rage nauyi) ta kasance awon sukarin jinin ta yana hauhawa akoda yaushe. Sakamakon haka, ƙwodar ta har ta kamu da cuta kuma an yi mata maganin ƙwodar. Ta riga ta rasa mahaifiyar ta da ‘yar’uwar ta sakamakon ciwon sukari.
Ta karbi shawarwarin mu a ranar 24 ga Nuwamba 2019 kuma ta sha alwashin cewa za ta bi duk shawarar da muka ba ta game da irin abincin da za ta kiyaye da kuma yanayin motsa jiki. Kwanaki 3 bayan haka, a ranar 27 ga Nuwamba, ta sanar da ni cewa ta auna sukarin jinin ta kuma ta samu 18.1 mmol / L (325.8 mg/dL). Sai na ƙara mata ƙarfin gwiwan ci gaba da sabon abincin da take ci. Bayan kwanaki 3, wato a ranar 30 ga Nuwamba, sai ta sanar da ni cewa ta auna sukarin jinin ta kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, ta samu 8.1 mmol/L (145.8 mg/dL) dududu kwanaki 6 kenan kacal bayan samun shawarwarin mu (24 – 30). Ta shaida min cewa tun bayan da ta kamu da cutar ciwon sukari, ba ta taɓa samun sukarin jinin ta ya yi kasa kamar 8.1 mmol/L ba wanda hakan ke nuna cewa ta dimin da’iman sukarin jinin ta yana hauhawa ne (hyperglycemai). Shawarwarin mu sun yi mata amfani tare da kwazon ta na ganin cewa ta bi abubuwan da muka shawarce ta da su sau da ƙafa.
“Ka wayi gari abincin ka ya kasance maganin ka, sannan kuma magani ya kasance shine abincin ka” – Hippocrates