Tare Da: Dr. Salihu Lukman
Gabatarwa
Idan nace babu abin da yake yamutsa mace, ya rikirkita ta, ya susuta ta, ta ji kaman ta dauki ranta, irin batun kishiya to ina ganin ban yi kuskure ba. A gani na, babu jarabawan da yafi girma ga ‘ya mace a wannan rayuwan irin a jarabce ta da zama da kishiya koda kuwa ba a gida daya suke zaune ba, wato kowacce da gidan ta. Idan mai karatun wannan qasidan namiji ne kuma yana tantaman wannan zancen nawa, to ya qaddara cewa su biyu ne maza a wajen matan shi, wato matan shi ta na aure da maza biyu, shi da wani daban! Wannan mummunan misalin, duk munin shi, abin da ke faruwa kenan ga mata. Duk yanda ka ke son ka kasance cewa kai kadai ne a cikin zuciyan matan ka, tofa ita ma haka take son kasancewa ita kadai ce a cikin rayuwan ka. Shin ko akwai macen da take son a yi mata kishiya saboda tana ganin cewa bata da kishi? A biyo ni a cikin wannan qasidan domin amsa wannan tambayan. Kishi yana daya daga cikin manyan abubuwan da suke sanadiyyar bayyanan Mental Disorder ga ‘ya mace saboda mawuyacin halin da suke samun kansu a ciki. Mata da yawa suna samun Depression (Major Depression Disorder) a lokacin da mijin su yake niyyar qara aure wanda kuma irin wannan halin da suke fadawa yana iya jefa su yin mugun aika-aika saboda Mental Health (lafiyan dabi’a) din su ya samu matsala babba tum ma ba idan kuma akayi rashin sa’an cewa Depression din nata ya hadu da ciwon tsananin so da bala’in kishi (Obsessive Love Disoder) ba.
Taqaitaccen Waiwaye A Kan Alamomin Depression (MDD) Da Obsessive Love Disorder (OLD)
A baya, na rubuta qasidu a inda na yi cikakken sharhi a game da yanda za ka gane mai dauke da Depression da kuma ciwon tsananin so da bala’in kishi (OLD). Zan lissafto alamomin wadannan disorders din ne kawai a nan qasa, domin mai karatu ya koma wadancan qasidun guda 2 wadanda zan yi ishara a kan su domin yin cikakken bita a kan wadannan Mental Disoders din.
Alamomin Depression guda 9 ne.
- Jin bakin ciki tare da yanke qauna ko kuma jin kawai kana son yin kuka a kusan kullum (depressed mood & hopelessness).
- Raguwan sha’awan abubuwan da da ka ke son yi wadanda suka shafi dukkanin harkokin ka a kusan kullum (anhedonia).
- Rashin cin abinci kaman yanda ka saba ko kuma cin abincin fiye da yanda ka saba ko kuma rage qiba ba tare da kana dieting ba ko qara qiba (change in appetite & body weight).
- Canji a yanda ka ke samun yin bacci a inda ka ke kasa yin bacci sosai yanda ka saba ko kuma kake yin baccin da ya wuce ƙima kusan a kullum (hypersomnia or insomnia).
- Jin kazar-kazar ko kuma ka ji ba ka son tabuka komai da jikin ka kaman kasala (psychomotor agitation or retardation).
- Rashin jin karsashi ko jin tsananin gajiya koda kuwa ba ka yi aikin da ya cancanci jin irin wannan gajiyan ba kusan a kullum (fatigue or loss of energy).
- Jin cewa ba ka da amfani ko kuma yawan zargin kan ka da kan ka (worthlessness or guilt).
- Kasa hada hankalin ka ko tunanin ka waje guda ko kasa yanke hukunci kusan a kullum (lack of concentration & indecisiveness).
- Yawan yin tunanin mutuwa, ko tunanin da ma ace ka mutu, ko kuma yunqurin kashe kanka (suicidal ideation or suicide attempt).
Sai aqalla 5 daga cikin wadannan alamomi 9 sun tabbata kuma sun wanzu har sati 2 cikakke koma fiye da haka sannan kuma dole daya daga cikin alamomin ya kasance #1 ko #2.
Domin cikakken sharhin wadannan alamomin, ka karanta maqala na mai taken, ‘Cikakken Bayani A Kan Yanda Za Ka Gane Me Dauke Da Depression (MDD) Ko Bipolar Disorder (BD)’.
Alamomin ciwon tsananin so da bala’in kishi wato Obsessive Love Disorder (OLD)
- Matsanancin qaunar mutum daya.
- Matuqar begen mutumin a koda yaushe.
- Ganin dacewan kare wanda ka ke so da tsare shi.
- Jin bala’in kishi akan shi.
- Jin cewa kai ba komi ba ne (low self-esteem).
- Tura saqonni kala-kala ta SMS, emails ko yawan kiran wanda suke so.
- Son a rarrashi mutum a koda yaushe.
- Wuyan yin abokai ko sada zumunci da sauran ‘yan’uwa saboda tsabagen maida hankali a wajen mutum daya.
- Bibiya da sa ido akan duk abubuwan da mutumin ya ke yi.
- Yunqurin juya mutum akan inda zai je da kuma abubuwan da zai iya yi.
Obsessive Love Disoder (OLD) ba yana tsaye ne da qafafun shi ba, yana bibiyan wasu Mental Disorders ne kaman Borderline Personality Disorder (BPD), Obsessive-Compulsive Disoder (OCD), Disinhibited Social Engagement Disorder (DSED), Obsessional Jealousy, da dai sauran su.
Domin cikakken sharhin wadannan alamomin, ka karanta maqala na mai taken, ‘Tsananin Fushi Da Bala’in Kishi, Me Yake Jawo Su? Borderline Personality Disorder & Obsessive Love Disorder’.
Halin Da Uwargida Ke Shiga A Sa’ilin Da Maigida Ya Yi Yunqurin Qara Aure
A mafi yawancin lokuta, mace na shiga wani matsanancin hali a sanda ta lura da cewa mijin ta yana da niyyar tafiya Qaraye wato qaro aure. Wannan yanayin yana jefa ‘ya mace a cikin damuwa wanda baya misaltuwa. Abin farko da ya ke fara fado mata shine mijin ta ya daina son ta ne shiyasa har zai iya yin mata kishiya wanda yasan cewa dole ranta zai baci a sabilin haka. Daga nan kuma sai ta tsunduma laluben abubuwan da takeyi domin ta nemo laifin da take yin mishi wanda har zai iya tunzura shi qara aure. A irin wannan yanayi, sai tsananin damuwa da yawan tunani da kishi su yi galaba a kan ta har ta iya shiga cikin matsanancin Depression a inda za ka ga cewa aqalla alamomi 5 daga cikin alamomi 9 na Depression wadanda na zayyana a sama sun bayyana a gareta. Wadanda suke da ilimin Mental Health wato lafiyan dabi’an dan Adam za su iya zuwa neman taimako wajen Psychiatrist a inda za a iya basu maganin Depression wato Antidepresseant saboda su sami sauqin halin da suka shiga ciki na ni ‘ya su. Wasu kuma sai kaga cewa sun qi neman taimakon likita a game da halin damuwan da suka shiga duk da cewa suna da tabbacin cewa alamomin Depression sun gama bayyana a tare da su, a irin wannan yanayin, sai kaga cewa mace tana ta ramewa tana lalacewa saboda bata iya yin bacci, bata iya cin abincin, wata ma bata iya yin aiki na gida ko kuwa na office. A taqaice dai duk wadanda suke kusantanta za su iya fahimtan cewa tana cikin wani mawuyacin hali. Wata kuma bata ma san alamomin Depression ba kwata-kwata koda kuwa tana dauke da shi saboda akwai qarancin ilimin cututtukan da za su iya shafan dabi’un mu wato Mental Disorders a cikin al’umman mu.
A wani lokacin kuma, idan kishin nata ya qarfafa sai kaga alamomin ciwon tsananin so da kishi wato Obsessive Love Disorder (OLD) wanda na lissafa a sama sun kunno kai. Wannan alamomin za su iya kunno kai tun kafin maganan qara aure ya taso, a wani lokaci kuma, yunqurin qara auren mijin ta shi ne zai qara tayar da Obsessive Love Disorder tuburan.
Daga nan kuma sai mace ta fara yawan yin leqen asiri a wayan mijin ta a inda za ta iya karanto ma kanta abin da zai iya hana ta sukuni har muddin ranta, ko kuma idan miji ya gano, ayi ta tashin hankali. Idan akayi rashin sa’a cewa shi ma mijin yana dauke da wani matsalan kaman Borderline Personality Disorder (BPD), to zai iya sakin ta saboda leqen asirin wayan shi kadai, kunga anan kenan, allura ta tono garma. Kun ga anan tsananin zafin kishi ya kashe mata aure kenan tun ma kafin amaryan ta shigo. Idan akayi rashin sa’an cewa itama tana dauke da BPD tare OLD sannan kuma da Depression ya lullube ta, za ta iya cewa za ta kashe mijin ta ko kishiyan ta ko kuma ta yi yunqurin kashe su ko kuma taci nasaran aika su barzagu ko kuma ta nemi kashe kanta. Kun ga aiki ya lalace kenan. Saboda da haka, dole maigida ya lura da wadannan alamomin na Depression, OLD da BPD da kyau, idan ba haka ba kuwa za ka iya wayin gari a lahira ko amaryan taka ko kuma ita uwargidan.
Shawara Zuwa Ga Maigida Mai Niyyar Qara Aure
- Ka sani cewa kishi dabi’a ce ta dan Adam. Saboda Allah (SWA) Ya bamu daman auren mata har guda 4 ba shi ke nuna cewa mata basu da kishi ba ko kuma mu yi tsammanin cewa idan sun nuna kishi a kan mu to kaman suna yin inkarin ayan da Allah Ya bamu daman qarin aure ne, a’a ba haka bane. Duk zurfin ilimin addini ‘ya mace ba ya hana ta yin kishi mai tsanani saboda shi kishi dabi’a ce ta dan Adam wanda ba ya bambanta na miji ko mace.
- Martaban kishin mata ya bambanta, wata kishin ta kadan ne har ma a iya yin tsammanin cewa kaman bata da kishi kwata-kwata, wata kuma kishin ta matsakaici ne wanda bai wuce gona da iri ba, sai kuma wanda nasu ya kai lahaula. A mafi yawancin lokuta za ka ga cewa wadanda nasu ya wuce na Shari’ah ya kai ga lahaula za ka ga cewa su na dauke da Mental Disorder ne, wadanda suke sahun gaba sune OLD da BPD.
- Dole ka kula da irin mawuyacin halin da matan ka za ta shiga a sanda ka ke qoqarin qarin aure sannan kuma ka tausaya mata iya iyawan ka wajen nuna damuwa da fahimta na yanayin da ta shiga wato Empathy. Idan ka ga alamomin Depression sun bayyana a gare ta ka dauke ta zuwa asibiti domin neman agajin Psychiatrist saboda kada yanayin nata ya gurbata har ya kai ga ta aikata wani mummunan ta’asa. Abin baqin ciki ne yanda za ka ga wasu mazajen suna nuna halin ko-in-kula ga matan su idan za su qara aure. Irin wannan halin yana qara musu damuwa sosai duk da yake kusan babu abin da maigida zai yi wanda zai kauda damuwan uwargida kwata-kwata in dai ba fasa auren ne zai yi ba gabadaya amma dai dole ya kwatanta.
- Duk tsiyatakun da matan ka za ta yi maka saboda aniyar ka ta qara aure kada ka sake ta. Wani yanayi suke shiga wanda su kadai suka san girman abun da ke damun su, saboda haka zata iya tunzura ka ta hanyoyi daban-daban akan ka sake ta amma ka yi haquri, ka jure, ka kauda kai kada ka sake ta koda kuwa ta maka ka a kotu domin haka. Za ka iya bata sararin shan iska kaman ta yi tafiya hutu a wajen iyayen ta ko kuma wani wajen daban domin ta dan sarara.
- Idan kuma kana so ka gajarce mata mawuyacin halin da zata shiga, to za ka iya boye mata neman auren da ka ke yi har sai dab da bikin sannan ka sanar da ita. A wannan yanayin, ka kashe tsuntsu 2 da dutse 1 kenan. Da farko ka rage mata tsayin lokacin da zata shiga kafin amarya ta shigo. Wasu mazan za ka ga suna neman aure har shekaru 3 koma 5 sannan kuma matan shi tana sane kuma tana cikin qunci a tsawon wannan lokacin har zuwa lokacin da amaryan za ta shigo daga ciki daga nan kuma a shiga Next Level na kishi. Na biyu, wasu matan suna iya shiga su fita har sai sun lalata auren da mijin su yake nema. Ka ga, a irin wannan yanayi, ba su ma sani ba ballantana su lalata maka neman auren ka. A lokacin da za su sani, zai kasance auren na ka yayi kusa sosai yanda ba za su iya samun daman yin komai ba. Amma fa a babin raha, idan kana so ayi maka binciken qeqe-da-qeqe kyauta a kan wanda ka ke son aura, to ka sanar da matan ka wanda ka ke son aura. Za ta shiga ta lalubo maka bayanai a game da ita kala-kala, kai kuma sai ka zurfafa ka tace bayanan nata. Kada ka rudu da cewa wai matan ka bata da kishi, saboda haka koda ka fada mata batun qarin auren ka tun da wuri ba za ta damu ba. Wasu matan za su iya nuna maka cewa suna tare da kai a kan qudurin ka dari bisa dari amma da zaran sun ga cewa da gaske ka fara shirye-shiryen shigowan wata, sai su canza gabadaya, ka kasa gane kan su kwata-kwata.
Sai mun hadu a kashi na gaba mai taken:
Shin Psychiatry Asibitin Mahaukata Ne? Wanene Likitan Kwakwalwa, Neurologist Ko Psychiatrist?
Salihu Lukman, Assistant Professor ne na Civil Engineering a University of Hafr Al Batin, Saudi Arabia