Part 5: Narcissist – Zuma Ga Zaqi Ga Harbi, Marmari Daga Nesa

Loading

Part 5: Narcissist – Zuma Ga Zaqi Ga Harbi, Marmari Daga Nesa

Tare Da: Dr. Salihu Lukman

(5) Aggressive/Sadist/Baiter/Hypersensitive/Paranoid

Daya daga cikin jiga-jigan alamomin Narcissists shine yanda suke da qarfin halin iya gasa ma mutum magana wato Bold and Contemptuous. A irin wannan yanayin, sai ka ji ana siffanta shi da cewa ai shi baya boye-boye, yana iya fada maka dukkanin abin da ke ranshi komai dadin shi, haka kuma komai dacin shi. Wannan na daya daga alamun rashin Empathy (na tattake wuri akan shi a baya qarqashin Part 2. Empathy ya qunshi abubuwa ne guda 2, Compassion (tausayi tare da jin damuwa na haqiqa akan mawuyacin halin da wani ya shiga) da Consideration (kara ko kawaici tare da sauqin hali). Narcissist ba shi da kara kuma bashi da ta’ido kwata-kwata, idan kuwa kaga ya nuna alamun Empathy, to a mafi yawancin lokuta yana da wata buri ne da yake son cimmawa, wato yana maida Empathy kaman makamin yaqin shi ne. A wajen gasa maganan shi, zai iya fadan abin da yake na raini ne ko na wulaqanci ko kuma barin zance amma shi ko a jikin shi, bai damu ba. Shi kuma yana da saurin tunzura akan abin da aka fada mishi wato Hypersensitive ko da kuwa maganan bata qunshi wani kalman batanci ba kwata-kwata. Wannan ya samo asali ne daga tsananin rashin yarda tare da tunanin cewa mutane sun tsangwame shi ko suna neman ganin bayan shi, wato Persecutory Paranoia. Narcissists ba sa gane-gane ko jiye-jiye (Psychosis) amma fa akwai su da jirkitar da abu daga asalin yanda ya faru zuwa yanda yayi daidai da son ransu domin su fara sakin wutan bala’i (Aggressive and Rageful). Narcissists sun kware wajen yin barin wutan fushin da idan mutum yayi nazari, sai ya ga cewa fushin bai dace ba gabadaya. Irin wannan yawan fusata da suke yi da diran ma mutane babu gaira babu sabab shi yasa wadanda suke kusa da su dole su dunga yin kaffa-kaffa da su kaman suna tafiya ne akan qaya (Walking on Eggshell). Irin wannan saurin fusatan, yana iya kaiwa ga duka, tun ma ba idan mijin ne Narcissist din ba, sai a dunga samun Domestic Violence ko kuma abin da ake kira da Intimate Partner Violence (IPV). Mafi yawancin masu yawan dukan matan su da zaran sun dan sami wani sabani Narcissists ne, idan kuma dukan ya kai ga rashin imani kaman ace dukan kawo wuqa kenan, to zai iya kasancewa ma Psychopath. Ku biyo ni kadan, zan yi qarin haske akan wai wanene Psychopath a qasa. Wasu matan fa wadanda suke Narcissists ne, suna iya dukan mazajen su idan wani abu ya hada su ko kuma su yi daka mishi tsawa, ko kuma su rife mishi qofa su hana shi fita ko kuma su biyo shi waje da gudu idan ya riga ya fita.

Masu irin wadannan siffan, sai ka ga cewa su fa ba sa jin dadi idan ba su yi rigima da husuma ba. Su ne rigima da mai amso musu abinci a gidan cin abinci, rigima da mai siyar da kaya a shago, rigima da mai duba takardun mota akan hanya, rigima da abokan aikin su ko mijin/matan su ko sauran wadanda suke mu’amala da su. Ma’ana dai shi ne, mafadata ne masu saurin hasala kuma rigimammu ne masu riqe da lamba 1 kuma mafi yawan masu mu’amala da su sun san hakan. Mai aure da irin wadannan idan sun shafe dan wani lokaci kaman sati 1 kila zuwa wata 1 ba tare da sun yi husuma ba, sai ya ji matan (idan ita ce Narcissist din) ta rakito wani abun da ya wuce da dadewa ko kuma ta qirqiro da wani batun da idan ya biye mata, za su yi husuma mai tsanani, wannan shine ake kira Baiting. Da zaran ka tanka mata, to, ka fada tarkon da ta dana maka kenan, daga nan kuma sai ka saurari luguden bala’in da zai biyo baya ko cin mutuncin da zai bata maka rai fiye da yanda ka ke tsammani. Baiting na daga cikin hanyoyin da Narcissists su ke bi wajen muzguna ma mutane. Hanyan kuwa da suke bi wajen aiwatar da Baiting din shine, za su dauko wani batu ne wanda za ka ga kaman ba shi da wani aibu, ko kuma batun da ba za ka iya hasashen cewa zai iya rikidewa daga qarshe ya zama sanadin husuma ko cece-ku-ce mai girma ba, da zaran ka tanka mata kuwa, to, ka rufta cikin ramin da fitan ka sai Allah sannan kuma sai ka yi nadaman tanka matan da ka yi daga farko. Idan kuma ta yi maka wani laifi har ka kai ga turke ta domin a maida magana na fahimta da nufin cewa kila ta gane laifin ta har ma tayi nadama tare da tuba, to fa ka dauko dutsen Dala da Goron Dutse duka a kan ka, saboda Narcissists ba sa taba yin nadama duk girman laifin da za ka kama su sun tafka ballantana su tuba ko su canza. Kai, sai dai ma su yi ta jayayya da kai a qoqarin wanke kansu da qarfi da yaji daga duk wani zargi wato Over-rationalization. Har sai kafi jin zafin hujjan da za su kawo domin kare kansu fiye da asalin laifin da su ka tafka maka. Saboda haka, domin zaman ka lafiya, karka taba turke ta ko ka yi jayayya da ita akan ko menene kuwa duk muhimmancin sa, idan ba haka ba kuwa, za ka yi babban nadaman yin haka daga qarshe. Guje ma duk wani tarko ko tattaunawa ko husuma da Narcissist musamman mata ne ko miji shine Dr. Ramani ta qirqiro kuma ta kira shi da sune Don’t DEEP Technique. Don’t DEEP yana nufin Don’t Defend (kada ka sake ka kare kan ka idan Narcissist ya taso ka gaba), Don’t Engage (kada kuma ka tanka mishi ma kwata-kwata, ka yi biris da shi kaman ba da kai yake magana ba), Don’t Explain (kada ka yi wani qarin bayani idan ya nemi qarin bayani daga wajen ka matuqar ka fassale mishi komai), Don’t Personalize (kada ka danganta matsalolin da ke faruwa a tsakanin ku cewa kai ne ummul’aba’isin faruwan su, a’a. Ainihin matsalan na ta’allaqe da Narcissist din, kuma babu abin da za ka iya yi domin ya daina baka matsala a rayuwan ka). Sauran hanyoyin datse illolin Narcissist sun hada da Gray Rocking/Firewalling da Soul-distancing, dukkanin su suna yin nuni ne ga mutum da ya janye jikin shi, ya rage yanda ya ke yin mu’amala da shi Narcissist din ta hanyar rage bude mishi cikin ka tare da yin takatsantsan din abin da za ka fada mishi. Kwatsam, sai na tuno da wasu baitoci 4 na waqen Imam Al-Shafi’i wadanda babban malamina, Mal. Maishago Zaria ya karatar da mu fiye da shekaru 20 da suka wuce a inda Imam Al-Shafi’I yake bada shawaran yanda za ka fuskanci mutumin da ya zo yin maka wargi a inda ya ke cewa:

إِذا نَطَقَ السَفيهُ فَلا تَجِبهُ (a)

فَخَيرٌ مِن إِجابَتِهِ السُكوتُ (b)

فَإِن كَلَّمتَهُ فَرَّجتَ عَنهُ (c)

وَإِن خَلَّيتَهُ كَمَداً يَموتُ (d)

(a) Idan wawa ya yi maka wargin zance, to kada ka tanka mishi.

(b) Saboda lallai yin shirun, shi yafi zama mafi alhairin amsan da za ka bashi.

(c) Idan da za ka amsa mishi (koda da baqin magana ne kuwa), to zai yi farin cikin hakan.

(d) Idan kuwa ka kyale shi kawai, to fa baqin ciki zai kashe shi.

Wadannan baitocin 4, sun tattaro kusan gabadaya abin da yake qunshe a cikin Don’t DEEP Technique, wanda sai bayan shekaru 1,300 sannan Dr. Ramani ta yi bincike mai zurfi sannan ta iya gano su a matsayin hanyoyin da suka fi dacewa ka mu’amalanci duk wani wawan da yake kawo maka wargi wanda ake kira a zamanance da suna Narcissist.

Shi fa Narcissist har alla-alla yake yi yaga cewa ya jefa ka cikin quncin rayuwa kuma zaka ga yana murna idan wani musifa ya same ka (Schadenfreude), wato shi mugu ne na gidi wanda ake kira da Sadist. Mafi yawancin wadanda za ka ga cewa ana siffanta su da sunan mugu bayan sun haura shekara 18, to da wuya su kasance ba Narcissists ba ne. Narcissist ya tattara duk wani mummunan dabi’an mu’amalan yau da kullum. Amma kuma duk muguntan shi, to Psychopath ya shige mishi gaba a ta wasu bangarorin. Idan mun fassara Narcissist da mugu to shi kuma Psychopath sai mu fassara shi da mara imani kwata-kwata. Psychopath ba Diagnosis ba ne, shima kaman Narcissist, ana siffanta mutum ne da Psychopath idan halayyan shi sun yi nuni ga cewa shi fa baisan abin da ya dace ba na mu’amalan yau da kullum, ko bin dokan hukuma ko kiyaye abubuwan al’adan mutane. Kuma duk wani tsaurin hukuncin da za a yi mishi na duka ko azaban wutan lantarki (Electric Shocking) ko zaman gidan maza wato Prison ba ya canza halin shi kwata-kwata. Misalin su sun hada da riqaqqun barayi da ‘yan fashi, da wadanda ake yin hayan su domin su kashe wani (Assassins), da masu faden mata sau da yawa (Serial Rapists), da masu satan mutane su kashe na kashewa su yi fade da wasun su (Kidnappers). Sun hada da wasu shugabannin kamfanoni (CEOs), a inda wani qididdiqa ya nuna cewa kowani 1 daga cikin 5 (5 – 21 %) na CEOs Psychopath ne. Daga cikin manyan bambance-bambance tsakanin Psychopath da Narcissist sun hada da: (1) Psychopath bai san mene faduwan gaba (Anxiousness) ba ma kwata-kwata kuma babu kalman Empathy ko tsoro (Fear) a cikin qamus (Dictionary) din shi. Kaman ace yayi kisan kai kuma gawan na motan shi, sai ya zo inda sojoji suke yin binciken motoci, duk da cewa akwai gawan da ya kashe a boye a cikin motan shi kuma za a iya kama shi amma bugun zuciyan shi ba zai canza ba sam, kuma koda an kama shi an yanke mishi hukunci ba zai ji nadaman laifin shi ba koda ya furta a baki, saboda da zai yiwu ya fito daga Prison din, to babu abun da zai hana ya sake tafta laifin da ya yi a baya. Tsarin da ke sa bugun zuciyan mutum ya qaru saboda ka yi wani laifi ko qarya shine ake kira da Autonomic Nervous System. Ko da za a saka ma Psychopath na’uran da yake gane mai fadan qarya (Lie Detector), ba zai iya kama Psychopath ba idan ya yi qarya saboda Autonomic Nervous System din shi daban ne dana sauran mutane. Shi kuwa Narcissist yana da Transactional Empathy kuma zai iya tsorata tare da samun faduwan gaba. (2) Shi kuma Psychopath ba ya neman yabon mutane ko qarfafawan su kwata-kwata, ba kaman Narcissist ba. Shi bai taba damuwa da abin da mutane za su ce a game da shi ba, sannan kuma illan shi ta fi na Narcissist girma. (3) A bangaren Diagnosis kuma, dakin su daban ne. Psychopath yana qarqashin Antisocial Personality Disorder (ASPD) ne shi kuma Narcissist yana qarqashin Narcissistic Personality Disorder (NPD) ne. Amma kuma a kashe-kashen Personality Disorders zuwa Cluster A, B da C, to gidan su daya ne domin dukkan su suna qarqashin Cluster B ne. Shiyasa wanda ake kira da Malignant Narcissist, wato Narcissist din da ya kasance Sadist ne kuma ya fi kowa yin illa ga mutane daga cikin sauran kashe-kashen Narcissist din, yana bambanta da Psychopath dan kadan ne kawai. Za ka iya siffanta bambancin su da gidaje ne guda 2 a hade wanda katanga ne kawai ya raba su. Akwai kuma wanda ke tsakiyan su shine ake kira da Sociopath, shi kuma dakin su daya da Psychopath, hasali ma qanin shine. Da Sociopath da Covert/Vulnerable Narcissist, katanga ne kawai ya raba su. Covert/Vulnerable Narcissist na daya cikin kashe-kashen Narcissist a inda yake daukan irin mutanen nan wadanda idan ka gansu a rana sai tausayin su ya lullube ka, ka jawo su cikin inuwa, ka ba su abinci da sutura, ka yi musu 10 ta arziki, amma kuma sai su nemi ingiza ka cikin ranan da ka fito da su ta hanyar cin dunduniyar ka a boye. Mafi yawancin Covert/Vulnerable Narcissists, Introverts ne. Alal misali, sai ka ga wata wanda masu riqon ta suke azabtarwa babu wani dalili, sai ka ji tausayin ta har ma ka nuna ko zata yarda ta aure ka domin ka raba ta da azaban da take ciki kuma ta yarda cikin dadin zuciya. Amma kuma bayan an yi auren, sai ta shigo maka da cikin shege a gida. Ka yi mata rana, ita kuma ta yi maka duhu. Allah Ya kyauta. Akwai Covert/Vulnerable Narcissists da yawa a cikin masu hidiman gida kaman masu aikin gida (House Maids), direba, mai gadi, da dai sauran su. Saboda yanda na yi arangama da masu halayyan Narcissists a cikin wadanda na taba dauka domin yin min aikin gida yasa na sha alwashin cewa ba zan qara daukan mai aiki ba, ko direba ko mai gadin da zai zauna a cikin gida, saboda idan kana da mata da yawa, to, irin wadannan za su dunga neman gwara kan su ne, kai kuma su qara maka matsalolin da suke kan ka kawai babu gaira ba sabab.

Saboda yanda alamomin Narcissist da Psychopath suke shiga cikin junan su, masu binciken halayyan dan Adam wato Psychologists suka qirqiro da Dark Triad (Narcissism, Marchiavellianism, Psychopathy) da kuma Dark Tetrad (Narcissism, Sadism, Marchiavellianism, Psychopathy). Sabon kalma anan kawai shine Marchiavellianism wanda yake nufin tsananin yaudara da ha’inci na Narcissist.

Yin samartaka ko zaman aure da Narcissist yana daya daga cikin manyan jarabawowin da Allah zai jarabce ka da shi. Saboda a mafi yawancin lokuta, shi Narcissist ba shi da juriyan yin alaqa mai dorewa kuma mai ingancin da ya wuce sati 6 zuwa 12, wato kaman wata daya da rabi kenan zuwa watanni 3 kacal. Wannan tsawon lokacin shine ake kira da Love Bombing ko Idealization, kuma wanda ke mu’amala da shi a matsayin budurwan shine ko kuwa har ma an yi aure, zata sha soyayyan da sai dai a mafarki ko kuma a littafan soyayya zata iya ganin irin shi. Domin kuwa sai ya dauke ta cif ya raba ta da wannan duniyan ta mu, ya kaita duniyar wata ta hanyoyin gwada mata soyayya da kula da damuwa da ‘yan’uwan ta da sakin hannu wajen yin barin kudi ko da kuwa talaka ne, saboda Narcissists ‘yan qarya ne na gidi. Duk hanyoyin da za su bi su burge mace, su saye imanin ta, sun san shi kala-kala. Ku tuna da bayanan da nayi a baya a game da 4C’s (Charm, Charisma, Confidence, Clever) a inda suke yin amfani da duk hanyoyin janyo hankalin wanda suke nema domin ya amince da su. Har ma ka ji ta na kiran shi da sunaye kaman My Soulmate wato rabin raina. Duk wanda ka ji an siffanta shi da Soulmate, to akwai babban ayan tambaya a wurin, domin da wuya ya kasance ba Narcissist ba ne. Saboda haka, da wuya Narcissists su iya yin samartakan (Courtship) da ya wuce watanni 3 daga nan kuma sai aure. Ko an yi auren, ko ba a yi auren ba, bayan kimanin watanni 3 sai a fada aji na gaba mai suna Devaluation. Anan ne fa mutumin zai fara ja da-baya-da-baya, sai ya fara dan saqa magana ko gasa magana tare da kushe wasu abubuwan da suka shafe ta. Sai ta fara shiga rudani, ta fara tunanin me ya sa ne saurayin ko mijin nan nata ya canza mata kwana biyu. Sai ta fara tunanin menene ta ke yi da ba daidai ba, ko kuma wasu hanyoyi ne za ta bi domin ta maida shi yanda yake a da. Matsala ya fara afkuwa. Wasu za su kasance a cikin wannan yanayin na Devaluation har illa masha Allah. Wasu kuma za su cigaba zuwa ajin gaba wato Discarding. A wannan ajin ne fa Narcissist din zai share ta kwata-kwata, ko ya rabu da ita ta hanyar katse  samartakan ko ya sake ta. A wani sa’in kuma, zai fita harkan ta ne kawai sai ya jira ta ta fara cewa bata son cigaba da auren ko samartakan daga nan sai ya labe da cewa ai ita ce ta fara cewa bata yi. Narcissist na son sabon abu a koda yaushe, shiyasa za ka ga cewa su so wannan, gobe kuma su kyale ta sannan su koma ma wata daban. Ko kuma su kasance auri saki, sai ka ji mutum ya yi aure gude 5 zuwa 10 kuma ya sake su daya bayan daya. Wasu na iya wucewa zuwa ajin gaba wanda ake kira da Hoovering wato yin biko. A nan ne za ka ga cewa Narcissist din ya yi randabawul, yana lafazin da zai taba tunanin matan da ya wulaqanta a baya ba tare da laifin ta ba. Duk wani kalma da aikin da yasan kina so, zai yi miki domin ki qara yarda da shi kuma ya cigaba da sauran abubuwan na shi na Idealization, sannan Devaluation sannan kuma Discarding. A wajen yin bikon, zai hada, da wasu alqawari da dama wadanda yasan cewa za su taimaka mishi wajen samun amincewan ki. Irin wadannan alqawarin sune ake kira da Future Fakes. Zai ce ba zai qara aikata abin da yayi ba, bayan qarya ne, zai cigaba ne kawai daga inda ya tsaya saboda Narcissist ba sa iya canzawa koda kuwa sun qudurce hakan a cikin ran su saboda haka dabi’an su yake, kuma bahaushe yace, hali zanen dutse, wato baka iya canza shi duk yanda ka so ka yi hakan. Wannan Karin maganan game da hali, ta fi shafan Narcissists da yayan shi Psychopath da kuma qanin Narcissist wato mai OCPD kenan. Zan tattake wuri a game da bambancin Narcissist da mai OCPD a qasan lamba (6) mai zuwa. Wadannan sune hanyoyin da Narcissist ya ke bi wajen cusguna ma wanda yake tare da ita a matsayin mata ce ko kuwa budurwan shi ce, wato, Love Bombing/Idealization, Devaluation, Discarding, Hoovering, da kuma Future Fakes. Wanda ya san Borderline Personality Disorder (BPD), zai ga cewa mai dauke da BPD ma yana siffantuwa da Idealization da Devaluation. Sai ka bibiyi tattake wurin da nayi a baya a qarqashin lamba (4), Part 4 kenan, a inda na fitar da bambance-bambance tsakanin mai BPD da Narcissist. Dole wasu alamomin su su kasance sun yi kama da juna saboda gidan su daya (Cluster B) amma kowa da dakin shi a cikin gidan, dakin BPD da dakin NPD.

Sai mun hadu a kashi na gaba a inda zan tattake wuri akan Red Flag na 6:

(6) Communal/Self-righteous/Cerebral Narcissist

Salihu Lukman, Assistant Professor ne na Civil Engineering a University of Hafr Al Batin, Saudi Arabia

Tagged : / / / / / / / /