Wata Dama Ta Magance Cutan Ciwon Sukari Da Wahalhalun Da Take Sabbabawa

Watanni 6 kenan da suka gabata.

Sakamakon sha’awar kawar da ciwon sukari a cikin al’ummarmu, mun kirkiro da DMF (Dandalin Kula da Mai Ciwon Sukari) akan WhatsApp (dandalin Hausa da Turanci) da Telegram (dandalin Hausa da Turanci), inda muka magance kalubalen da ke tare da kula da ciwon sukari tsakanin mambobi. Tare da taimakon likitocinmu, an ƙarfafa ma mambobi gwiwan cike wani nau’in takarda (form) na musamman don taimaka mana fahimtar yanayin rayuwar su da kuma ba su tabbatattun shawarwarin da zai taimaka musu wajen gudanar da yanayin ciwon sukarin su ta hanyar da tafi dacewa. Sakamakon haka – mun sami labarai na cin nasara daga mambobin mu marasa iyaka!!! Domin mu sami daman taimaka muku taimakawa mafi kyau, mun ƙirƙiro da wani babban tsari wanda ake biyan kudi a inda zamu kasance tare da ku a kullum wajen ganin cewa kun cimma burinku na rabuwa da wannan cutan.

 

Yanda Shirin Zai Kasance

Shirin zai kunshi ayyukan da za a dunga yi a kullun ciki har da awon sukarin jini sau da yawa, ire-iren abincin da yakamata a ci (gami da tsarin girke-girke wato recipes, idan da buƙata) da magunguna ko allura (idan da buƙata). Bibiyan wannan tsarin zai kasance ta hanyar cike fom a kullun da kuma sadarwa ta waya, a inda buƙatan hakan ya kama. Babban hanyar sadarwar zata kasance ne ta sashin sada zumunta na DMF group a kan yanar gizo.

Abubuwan Da Ake Da Buƙata Kafin A Fara Wannan Sabon Shirin

(1) Mallakan na’uran awon jini wato glucometer (samfurin da aka fi ba da shawara shine: Accu-Chek Active) tare da isasshen abin da akeyin gwajin da shi wato strips wanda za su isa har zuwa tsawon lokacin da aka zaba.

(2) Gwagwajen asibiti wadanda suka shafi lafiyan aikin ƙoda, zuciya, hanta da idanu.

(3) Gwajin glycated haemoglin domin sanin awon sukarin jini a cikin watanni 3 da suka gabata.

(4) Ganin cewa shirin ya ƙunshi cikakken sauyin abinci, duk wanda zai shiga wannan tsarin ya kamata ya tanadi kudaden da za su ishe shi domin cimma burin da ake so na fatattakan ciwon sukari.

Sakamakon Da Ake Fatan Samu Bayan Kammala Wannan Shirin

(1) Samun kyakkyawan sakamako na awon sukarin jini a ƙarshen wannan shirin tare da yuwuwar barin shan magunguna ƙwata-ƙwata (wanda za a fi dacewa da samun hakan a ƙarƙashin shirin watanni 3) da kuma cikakkiyar waraka daga ciwon sukari ko kuma sauran matsalolin da ciwon sukarin ke kawo wa kamar rashin sha’awa ko kuzari ga ma’aurata, lalacewar ƙafa, rashin gani da kyau, lalacewar koda, da dai sauransu.

(2) Tsarin abinci mai ɗorewa wanda zai ba da tabbacin rage nauyi mai lafiya – rage nauyi yana da mahimmanci a cikin ingantaccen sarrafa wasu cututtuka kamar ciwon hawan jini, cututtukan jijiyoyin zuciya, cututtukan ƙwayar haihuwa na mata (PCOS), amosanin gaɓɓai, da dai sauran su.

Kashe-kashen Farashin Kowane Zango

Cancanta

  • Masu nau’in ciwon sukari mai suna type 2.
  • Masu ƙiba sosai, wadanda suke neman rage ƙiba.

A Tuntube Mu

Don ƙarin bayani, gami da bayanin biyan kuɗi, tuntuɓi:

Wayan Salula: +2349052837957 (saƙon WhatsApp kadai)       +966501968813 (kira kadai)

Adireshin imel (Email): dmf@salihulukman.com                                   

Yanar gizo: salihulukman.com/dmf



Tagged : / /

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *