Amsoshin da na ba wani a game da ciwon aljanu

Loading

Tare Da: Dr. Salihu Lukman

Mai sharhi: “Ba ina kore abinda kake da’awar shi ba amma bayanen ka ya nuna baka da ilmin ruqya a karkashin koyarwar masana da halayyar Aljanu.”

Amsa ta: Da’awar ka na cewa ba ni da ilmin ruqya a karkashin koyarwar masana da halayyar aljanu ba gaskiya ba ne. Daga jin zancen ka, baka sanni ba kuma baka san tarihin karatuna ba a wannan fagen. Ba wai ina cewa ni wani malamin ruqya ba ne, amma na sami horaswa akan ruqya daidai gwargwado tun sanda batun ruqya ya fara yaduwa a cikin mutane wato wajen 93-94, ban sani ba ko an haife ka a wannan lokacin saboda na ga kaman kai matashi ne.

Na fara samun horaswa na ilimin aljanu ne a wajen Mal. Idris Salihu wanda ke Kwarbai a cikin birnin Zaria wanda daga bisani limamin mu wato Mal. Ahmad Harun (limamin masallacin Dansabo wanda take a Lemu Zaria City) ya qara mana wannan ilimin tare da dabbaqawa. Wannan duk ya faru ne a tsakanin 93-95 muna matasa. Daga baya kuma da na fara halartan karatuttukan marigayi Mal. Albani Zaria wanda yafi kowani malami shahara wajen yada ilimin aljanu a Zaria a iya sani na. Shima ya karantar damu littafin ruqya wanda a lokacin itace littafin da tafi kowane littafi yin bayani akan ruqya wato Assarimulbattar sannan kuma ya hada mana da Wiqayatul Insan duka na Wahid Abdussalam Bali. Wannan bayan ya yi ta yin seminars a Kongo Campus a inda yake qara ilmantarwa a game da aljanu da ruqya tare da yi a aikace. Duk wadannan karatuttukan za ka iya samun su a YouTube channel dina: https://www.youtube.com/@drsalihulukman
A baya bayan nan, Mal. Maishago na Magume Zaria ya hada ni da Mal. Ayuba na Gidan Kwano. Mal. Ayuba ya kasance yaron Mal. Abubakar Gidan Zuma, Kongo Campus, kuma yana daya daga cikin mashahuran masu yin ruqya a Zaria kuma na lizimce shi sosai a inda na qara ilimin aljanu da kuma ruqya a wajen sa.
Saboda haka cewa da kayi wai bani da ilmin ruqya a karkashin koyarwar masana da halayyar Aljanu wannan iqirarin shashi fadi kawai ba shi da tushe. Da ma dai ace ka tambaye ni ne in fada maka karatun da na yi akan ruqya da halayyar aljanu da yafi dacewa akan yanda ka yi amfani da cewa na kawo wani abu wanda kai ka ke ganin ba haka ba ne ka yanke hukuncin cewa bani da ilimin abun ne bayan na yi tsokaci a cikin rubutu na cewa nima a kafin wannan binciken da na gano ina yin ruqya. Ina yin ruqya kimanin shekaru 28 da suka wuce. Kuma na kai wasu daga cikin ‘yan’uwa na wajen mashahuren masu yin ruqya a Zaria domin a cire musu aljanu. Saboda haka, ina da masaniya sosai akan ruqya da kuma duniyan aljanu.

Mai sharhi: “Shawara akan haka idan kana da wani nazari da kayi ko kuma kake so ka tabbatar da ra’ayin wasu mutane ka tsaya ka bayyana ra’ayin ka ba sai ka kore abinda ilmi da gwaji ya tabbatar da shi ba”

Amsa ta: Ka sani da cewa duk abubuwan da na rubuta a wannan post din, ra’ayi na ne ba na wani ba. Ba dakon ra’ayin wani nake yi ba. Tun sanda batun shigan aljani jikin mutum ya shahara (93-94), wasu mutane har ma da malamai sun qi yarda da abun kwata-kwata amma ni duk wanda ya sanni zai baka shedan cewa ni ada na gamsu da ciwon aljanu kaman yanda ake siffantawa. Daya daga cikin mata na wanda take kwararriyar likita ce ta taba fada min a shekarun baya cewa duk alamomin da ake siffanta masu ciwon aljanu da su, to likitancin Psychiatry na da ta cewa akan su. A lokacin da ta fada min wannan maganan sai na ji ban yarda ba kawai saboda a lokacin ina ganin cewa babu abin da zai iya gamsar dani a game da ire-iren abubuwan da masu ciwon aljanu suke yi idan ba ciwon aljanun kanshi ba. Sannan kuma a lokacin na kasance ba ni da wani ilimin halayyar dan’Adam wato Psychology sannan kuma ilimina a kan Mental Disorders bai taka kara ya karya ba.

Amma daga baya, da na tsunduma yin bincike a game da Psychology da kuma Mental Disorders, ni da kaina na ci karo da wannan Dissociative Identity Disorder din. Bayan zurfafa bincike akan shi sai na gano cewa lallai shine Multiple Personality Disorder (MPD) wanda mata ta ta taba fada min a shekarun baya wanda a gaskiya ni na ma manta cewa ta taba fada min komai a game da MPD.

Saboda haka, wadannan abubuwan dana gabatar duka abubuwa ne wanda ilimin zamani na Psychiatry suka tabbatar da su babu wani tambaba. Amma bance dole sai ka yarda da abin da na fada ba kamar yanda nima a baya na qi yarda da abin da mata ta ta fada min a game da ciwon aljanu har sai da na yi bincike na na gano hakan ni da kaina, kaima ina baka shawaran cewa ka zurfafa bincike a game da Mental Disorders ko da kuwa zai kama ka tuntubi Psychiatrists ne ko kuma Clinical Psychologists akan batun. Ilimi yana da matuqar fadi.

Har yanzu mutanen mu basu karbi likitancin zamani ba yanda ya kamata. Har yanzu wasu daga mutanen mu ba sa son zuwa asibiti sai abu ya baci tukuna wasu kuma har sai sun kusa kaiwa gargara. Imanin mutane a kan lafiyan su ya fi tafiya wajen masu bada maganin gargajiya. Ba ina cewa kada mutane suje wajen masu maganin gargajiya bane a’a, amma dole musan matsayin da za mu ajiye ko wannen su. Masu maganin gargajiya wadanda suke da tsantseni za ka ga cewa idan ka je musu da wani matsala, za su ce maka ka fara zuwa asibiti ayi maka gwaje-gwaje idan kuma abin ya ci tura to sai ka zo wajen su domin suga abin da za su iya yin maka. Ina kyautata zaton cewa da yawa daga masu bada maganin gargajiya a yanzu ba sa yin haka. Abin har ya kai ga wasu masu maganin gargajiya za ka ji su suna da’awar cewa wai suna bada maganin waraka daga Cancer, HIV, Hepatitis B, Kidney, Sickler da dai sauran manyan cututtukan da har yanzu ba su da magani a likitance. Idan da da gaske ne suna warkarwa daga wadannan cututtukan da suka addabe mu to ai da yau babu sauran mai dauke da wadannan cututtukan a NIgeria. A yawancin lokuta, suna fakewa da cewa maganin su yana da NAFDAC Registration, sai su yi nuni kaman ai har ma NAFDAC ta tabbatar da ingancin maganin su. Mutane su sani cewa abin da NAFDAC kadai take yi shine tabbatar da cewa mutum zai iya amfani da maganin ba tare da maganin ya cutar da shi ba kadai. Alal misali, idan ance wannan maganin sickler ne, to abin da NAFDAC zata yi kawai shine ta gwada magani ta gani cewa ba zai yi ma mutum illa ba idan ya sha amma ba za ta gwada maganin ba akan wanda yake da cutan sickler ta gani cewa ko zai warke daga ciwon ba. Mutane ya kamata su gane wannan. Mutane ya kamata su rungumi likitancin zamani da kyau saboda ni a gani na ma yana daya daga cikin mu’u’juzozin manzon Allah (SWA). Duk da yake a zamanin sa babu irin wadannan cigaba da muke da shi na wannan zamanin amma kuma a zamanin al’umman Annabi Muhammadu ne kawai aka samu wannan cigaban shiyasa zaka ga yawancin qasashen musulmai sun rungumi likitancin zamani sosai ba tare da wani kyama ba. Na ga cewa kana yin karatu ne a Dubai, ban sani ba ko ka taba ganin shagon maganin gargajiya a can. Tsawon shekaru 12 da na yi a Saudiyya, ban taba ganin shagon maganin gargajiya ba har ila yau. Mu kuwa a Nigeria ka ce mune cibiyar yada maganin gargajiya na duniya. Allah Ya sa mudace, amin.

Salihu Lukman, Assistant Professor ne na Civil Engineering a University of Hafr Al Batin, Saudi Arabia



Tagged : / / /

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *