Ciwon Aljanu Ne Ko Kuwa Dissociative Identity Disorder?

Loading

Tare Da: Dr. Salihu Lukman

Ina so in dan yi ma mutane ne wani tsokaci a game wasu cututtukan halayyan dan’Adam wato Mental/Psychiatric/Psychological Disorders wadanda yawancin mutane suke dangantawa da cewa aljani ne ya shiga mutum ko kuma a wasu lokutan ace an yi ma mutum sammu ko sihiri.

Ku sani cewa ba wai ina so in ce babu duniyar aljanu ne ba kwata-kwata ko kuma in ce aljani ba zai iya shiga jikin dan’Adam ba, a’a. Abin kawai da ni ke so in tabbatar a nan shine su wadannan cututtukan wanda zan ambato su a qasa likitocin halayyan dan’Adam (Psychiatrists) sun tabbatar da cewa wadannan cututtuka ne wadanda suka shafi halayyan mutum wato Mental Disorders kuma wasun su ma suna da maganin zamani na asibiti wanda idan mutum ya sha zai iya warkewa ko kuma samun sauqi, wasun su kuma Clinical Psychologists ko kuma Therapists ko kuma Psychiatrists wadanda suka sami horo a bangaren Psychotherapy za su iya warkar da mutum ko kuma su koyar da kai hanyoyin da zaka iya rage illolin abin da ke damun ka. Akwai qarancin wadannan kwararrun a Nigeria sosai.

Mutane suna da wani dabi’a na danganta wa aljani ko kuma sihiri duk wani abun da suke ganin cewa ya saba ma hankali da kuma dabi’a ta dan’Adam ko kuma bako ne. Alal misali, a da ana cewa cutan shan Inna wato Polio cuta ce wanda aljani ko aljana mai suna Inna ya/ta ke shafan mutum har ya/ta saka mai cutan a inda daya daga cikin qafafuwan mutum zai shanye ya kasa sarrafuwa. Daga baya, sai likitoci suka tabbatar da cewa cutan shan Inna ba aljani ne ke kawo shi ba, wata kwayar cuta ce mai suna Poliovirus wanda a halin yanzu kusan an kawar da cutan a Nigeria dama sauran qasashen duniya.

Mental Disorders din da zan yi dan tsokaci akan su ba irin Polio ba ne wanda wata kwayan cuta ke jawo wa. Su Mental Disorders cututtuka ne wadanda ake samu ta gado wato Nature/Genetics ko kuma yanayin muhallin da mutum ya taso ko kuma abubuwan da suka faru da mutum yayin girman sa wato Nurture.

(1) Dannau (Sleep Paralysis): Dannau dai wani yanayi ne wanda mutum ke shiga a bacci sai ka ji ka dan farka amma kuma ka kasa motsi kwata-kwata kaman an danne ka, tare da zufa da numfashi sama-sama, a wani lokaci ma har da sleep-related hallucinations wato jiye-jiye ko gane-gane wanda bayan dan wani lokaci (daqiqai zuwa minti 2) kuma sai ka dawo daidai wato sai ka iya motsa gabban jikin ka kaman wanda ya danne ka din ya tafi.

Wannan shine ake kira Sleep Paralysis, kuma mafi yawan lokaci yana kama mutanen da ke dauke da wadannan Mental Disorders din ne kaman insomnia, narcolepsy, depression, anxiety disorders, bipolar disorder, post-traumatic stress disorder (PTSD).

Domin cikakken qarin bayani a kan dannau da kuma yanda ake maganin shi, ka bibiyi wadannan hujjojin a qasa:

(i) Bidiyon Dr. Maryam Almustapha: https://www.youtube.com/watch?v=vSGyTxoOADY

(ii) https://www.healthline.com/health/sleep/isolated-sleep-paralysis

(iii) Diagnostic & Statistical Manual of Mental Disorders, 5th edition, DSM-5 (American Psychiatric Association). Page 375. https://t.me/elibrary_mobile/6658

(2) Shigan Aljani Jikin Mutum Ko Kuma Shafan Aljanu: Ana cewa aljani ya shiga mutum ne ko kuma ya kama shi idan wani lokaci mutum ya kan shiga wani halin da tabi’an sa da yanayin sa tare muryan sa duk sai su canza. Sai kaga mutum yana magana da muryar da ba a sanshi da shi ba. A wannan yanayin sai ace wai aljani ne ya kama shi kuma ma aljanin ne yake magana a bakin shi mutumin. Haka ko na iya faruwa ne haka kawai ko kuma a sa’ilin da ake karantawa mai ciwon Al-Qur’ani wato Ruqya. A lokacin yin Ruqya, ana iya yin magana da su wadanda ake zaton wai aljanu ne wadanda ke jikin mutum ko da kuwa suna da yawa. Wani lokaci za a ce mutum yana da aljanu 2, 5, 10, ko kuma ma fiye da haka sannan kuma duk sanda daya daga cikin aljanun ya halarto mai, to yanayin shi gabadaya zai canza, wani lokaci, zai san me ya ke yi a wani lokaci kuma ba zai tuna komai ba har sai ya dawo cikin hayyancin sa. Mutum zai iya yin tafiya zuwa wani wuri kaman ace ya tashi daga gidan shi zuwa kasuwa ko kuma wani gari daban amma kuma sai ya kasa tuna yanda akayi har ya yi wannan tafiya sai ace ai aljani ne ya dauke shi ya kaishi wajen. Hakazalika, za ka iya ganin kayayyakin kasuwa amma kuma ba za ka iya tuna sanda ka tafi kasuwan ba kayi siyayyan kayayyakin, sai ace wai aljani ne kawo maka. Makuwa ma tana iya faruwa da mutum. Sannan kuma za ka iya yin jiye-jiye na maganganu ko kuma gane-gane (hallucinations). Wani yana iya neman cutar da kansa ta hanyar azabtar da kansa ko kuma neman kashe kanshi idan ya shiga yanayin da ake ganin cewa aljani ne ya halarto shi. Da yawancin mutane sun tafi akan cewa ire-iren wadannan alamomin da na lissafta alamomin cewa aljani ya shiga jikin mutum kuma shine yake saka shi yake yin irin wadannan ayyuka.

Amma da na zurfafa bincike a kan cututtukan da suka shafi halayyar dan’Adam wato Mental Disorders sai na gano cewa abin da muke kira da ciwon aljanu ko kuma shafan aljani ba komai bane face wata Mental Disorder ne wanda likitocin halayyar dan’Adam (Psychiatrists) ke kira da Dissociative Identity Disorder (DID) wanda ada ake kira da Multiple Personality Disorder (MPD) ko kuma Split Personality Disorder (SPD). Yawancin mutanen da suke dauke da DID za a ga cewa suna kuma dauke da wasu Mental Disorder(s) abin da likitoci ke kira Cormobidity kaman PTSD, depressive disorders, personality disorders, da dai sauran su. Idan mutum yana da wannan cutan, to ya garzaya asibiti domin ganin Psychiatrist wanda zai duba yanayin da kake ciki domin maganin abubuwan da kake ji. Likitan zai iya baka magani ko kuma ya sa ayi maka Psychotherapy. Akwai turawa ma da yawa wadanda suke tattare da wannan cutan, saboda haka wannan ba cuta bane ta take shafan Musulmai kawai kaman yanda wasu ke tsammani. Kafin in gano Dissociative Identity Disorder, nima ina yin Ruqya ga wanda ake zaton cewa aljani ya shafa. Kuma an sha yin magana da aljani (alter) a gabana. Amma a yanzu na gane cewa a hakika ba aljani bane ake magana da shi, yanayin mutum ne wato personality ne kawai yake canzawa sai a dauka kaman cewa aljani ne ya hallaro. Ku gane cewa ba ina cewa babu aljani bane kwata-kwata, ko kuma ina cewa aljani ba zai iya shiga jikin mutum ba, abin kawai da ni ke so mutane su gane shine, abin da muke kira da ciwon aljani ko kuma shiga ko shafan aljani to ba komai bane illa wani Mental Disorder ne mai suna Dissociative Identity Disorder kamar yanda a da ake cewa dannau aljani ke danne mutum wanda daga baya Psychiatrists suka gano cewa a hakika ba aljani ba ne kawai wani alama ce ta Mental Disorder wanda ake kira da Sleep Paralysis. Abubuwannan suna da matuqar mamaki amma kuma ku gane cewa duk inda muke tsammanin kwakwalwar dan’Adam ta kai to ta wuce nan. Tana da abin ban mamaki sosai.

Domin cikakken qarin bayani a game da Dissociative Identity Disorder wato abin da ake kira ciwon aljanu da kuma yanda ake maganin shi, ka bibiyi wadannan hujjojin a qasa:

(i) Bidiyon da akayi fira da wata mai ‘aljanu’ (alters) 11 kuma daya daga cikin ‘aljanun’ ta hallara a yayin firan: https://www.youtube.com/watch?v=A0kLjsY4JlU

(ii) Bidiyon Dr. Ramani Durvasula a game da DID: https://www.youtube.com/watch?v=_i-p3g3Epm8

(Iii) https://www.healthline.com/health/dissociative-identity-disorder

(iv) Diagnostic & Statistical Manual of Mental Disorders, 5th edition, DSM-5 (American Psychiatric Association). Page 292. https://t.me/elibrary_mobile/6658

(3) Sammu/Sihiri: Na yarda cewa za a iya yin ma mutum sihiri ko sammu kuma ta kama shi da ikon Allah. Amma abin da na lura da shi shine, mutane suna da saurin cewa an yi ma mutum sihiri da zaran yanayin wasu abubuwa na daban da bai saba yi ba ko kuma idan dabi’ar sa ta canza akan mutane ko kuma akan aikin sa ko karatun sa. Ga misalai akan haka:

(a) Wanda ya gudu daga wajen aikin sa ko makaranta, ko kuma ya daina zuwa aikin/makarantan kwata-kwata, ko kuma sai ya je wajen aikin/makarantan amma kuma sai ya kasa yin aikin/karatun gabadaya, ko kuma mutum ya daina fita waje kwata-kwata ya maqale a dakin shi a koda yaushe kuma baya son shiga jama’a sannan ga qazanta ko kuma yawan bacci ko rashin bacci. Ko kuma mutum yayi ta ciwon jiki, kai, ko ciki amma kuma duk gwajin da akayi a asibiti bai nuna wani cuta ba. Mutane suna da saurin alaqanta wadannan alamomi da cewa an yi ma mutum sammu ne alhali akwai tarin Mental Disorders din da za su iya sa mutum aikata duka wadannan ayyukan kaman depressive disorders, bipolar disorder, borderline personality disorder, schizoid personality disorder, somatic symptom disorder, da dai sauran su. Idan ka ji daya daga cikin wadannan alamomin, to kai yi marmaza ka garzaya asibiti wajen Psychiatrist domin a duba a gano abin da ke damun ka domin ayi maka maganin da ya dace kafin abubuwan su tabarbare.

(b) Mutum ya dunga jin maganganu ko kuma gane-gane (hallucinations), tare da magana mara kan gado ko da sauri-sauri sannan da jin kai (grandiosity) ko kuma yarda da abin da ba zai yiwu ba (delusion) kaman mutum yace shi Mahdi ne wanda zai zo qarshen zamani, da dai sauran dabi’u mara kan gado kaman kashe-kashen kudi ba tare da tunani ba, ko kuma aikata wasu ayyukan da za su iya kawo ma mutum illa. Wanda ya ji irin wadannan alamomin ko kuma ya ga wani na kusa da shi yana dauke da wadannan alamomin to sai ya garzaya asibiti wajen Psychiatrist domin neman magani saboda akwai Mental Disorders da yawa da za su iya jawo wadannan alamomin kaman schizophrenia, bipolar disorder, da dai sauran su. Schizophrenia ta na daya daga cikin cututtukan da suke sa mutum ya koma mahaukaci tuburan idan dai har ba a yi maganin ta ba. Wasu daga cikin wadannan Mental Disorders idan ba a yi maganin su ba za su iya sa mutum ya yi tafiya akan titi tsirara ko kuma ya dunga dukan mutane ko kuma ya dunga sunbatu. Saboda haka a kula. A madadin da anga irin wadannan alamun a ce ai sammu ne, gara ayi marmaza a garzaya asibiti domin neman magani.

Daga qarshe, ka sani cewa mutane ba sa son zuwa ganin Psychiatrist saboda gudun ace sun haukace daga baya ayi ta yi da su wato stigma. Ka sani cewa shi Psychiatrist yana duba daga mai ciwon kai har zuwa wanda ake ganin cewa mahaukaci ne tuburan. Saboda haka, da zaran mun ji ba daidai ba a yanayin yanda muka saba ayyukan mu a wajen aiki ne ko kuwa a gida ne ko kuwa a alaqar mu ne da sauran mutane, to mu yi sauri mu tafi wajen Psychiatrist saboda a duba mu. A lokuta da dama, masu Mental Disorders ba sa son kai kansu wajen likita domin ya duba su, saboda haka, dole wanda yake jibintar lamarin su ko kuma yake kusa da su kaman uba, uwa, miji, mata, yaya, aboki da dai sauran su su kula sannan suyi abinda ya dace wajen garzayawa asibiti da zaran anga cewa akwai buqatan haka.

Salihu Lukman, Assistant Professor ne na Civil Engineering a University of Hafr Al Batin, Saudi Arabia

 

 

 



Tagged : / / /

One thought on “Ciwon Aljanu Ne Ko Kuwa Dissociative Identity Disorder?

  1. Madallah. Munji bayani. Amma ina ganin akwai abun da baka fahimta ba game da complexity na sha’anin aljanu da sihiri a jikin dan adam. Duk mun yarda abubuwan da ka lissafo na disorders a personality duk yana iya faruwa da mutum medically under normal medical condition da zaa iya treating nasa da maganin asibiti. To amma sai ka gane kuma wadannan disorders din na personality sune dai hanyoyin da aljani ko sihiri yake yin tasiri a jikin mutum. Ka kara fahimta cewa daman aljani ko sihiri ai suna taking over normal personality na mutum ne sai ya zama na anyi exposing nasa zuwa ga personality disorders wanda daman hakan shine makasudin wannan shafar aljanin sihirin dake jikin mutum.

    To idan aka samu kwararren da yasan meye aljani da sihiri kuma yasan meye psychotherapy na spritual dana medical to yasan hanyoyin da zai yi diagonisng ya gane cewa wannan disorders na medical issue ne ko spritual.

    A karshe ina ganin ka kara zurfafa bincike sosai musamman cikin rubuce rubucen sigmund freaud na psychoanalysis, duk da cewa shi ba ta fuskar tabbatar da batun aljani ko sihiri yayi ba amma nazariyar sa tana kara tabbatar da samuwar shafar aljani da sihiri ne a jikin mutum. Allahu A’alam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *