Table of Contents
Narcissist (2) – Zuma Ga Zaqi Ga Harbi, Marmari Daga Nesa
Tare Da: Dr. Salihu Lukman
(1) Gaslighting/Lack of Guilt/Lack of Insight/Never Takes Responsibility/Lying
Samun kan ka cikin buqatuwan ajiye saqonnin ka tsakanin ka da mutum kaman text message (saqon kar ta kwana), e-mail, ko kuma WhatsApp chat (hiran WhatsApp) domin nuna mishi nan gaba idan ya qaryata abin da ku ka tattauna da shi na daya daga nau’in rainin hankali. Wannan halin yana shafan mu’amala da mutumin da yake yawan qaryata abin da ya fada a baya ko kuma yayi qaryan cewa ya fada maka wani abu a baya alhali kuma ba haka abin yake ba. Zai iya dora ma laifi akan abin da baka-ji-ba baka-gani-ba ko kuma yayi maka qage ko kuma ya iyar da lamarin sabanin haqiqanin yanda ya faru domin cimma wani buri daban nasa ko kuma domin ya bata ka. Irin wadannan abubuwan da za su sa ka koma yin nazari a game da abin da aka fada maka domin ware zare da abawa ko kuma ka ji kaman kan ka zai buga saboda takaici da rudani ana kiranshi da Gaslighting. Gaslighting wani karatu ne mai zurfi kuma mai matuqar amfani wajen fahimtar Narcissist kuma ya karkasu har gida 4 kamar haka: Minimization, Blame-shifting, Deflection, da Projection. Ga kadan daga cikin jumlolin da Gaslighter zai iya amfani da su wadanda suke nuna rashin nadama akan laifin da akayi (Lack of guilt) ko kuma rashin fahimtar girman laifin kan shi (Lack of insight):
- Wannan ai ba kayan gabas bane wato ba komai bane ko ya nuna cewa kana daga hankalin ka akan abin da bai kamata ba (alhali abu ne babba wanda duk mai tunani zai bashi muhimmanci sosai. Babban misali anan shine kaman ace miji ya kama matan shi tana yin hulda da tsohon saurayinta ta hanyar text message, ko kiran waya, ko WhatsApp Chat, to sai ya nuna bacin ran shi akan haka. Ita kuma sai kawai ta nuna cewa babu komai yana tayar da hankalin shi ne akan abin da ba komai bane.).
- Ban taba yin abu kaza ba (bayan ya sha yin abun shaye-shaye ma).
- Ai laifin ka ne da baka yi abu kaza-da-kaza ba shi yasa na aikata abu kaza-da-kaza (kaman miji ya kama matan shi tana karban rage hanya (Lift) daga mutumin da bata san shi ba sai ya tsawatar mata amma sai ta maida mishi da martanin cewa ai laifin shi ne da bai siya mata mota ba. Ko kuma mata ta kama mijinta yana yin lalata da mai aikin ta ko qanwarta idan ta je wajen aiki ko kuma da dare sai ya ce mata ai laifin ta ne da ba ta ba shi isashshen lokaci shiyasa yake neme-nemen mata).
- Ina murnan cewa zan koma wajen shanu da tumakaina saboda sun fi mutane sauqin sarrafawa (irin wannan kwatancen a inda za a hada dabbobi da ‘yan Adam kuma a nuna cewa wai sun fi sauqin sarrafuwa ba qaramin Gaslighting ba ne saboda zai jefa mutum cikin tunani kala-kala domin gano yanda dabbobi za a iya fifita su akan mutane da wannan lafazin).
- Tun da muke da kai ba ka taba yin mini wani alkhairi ba (alhali kuwa ka sha yin mishi alkhairin da basu qirguwa)
A mafi akasarin lokuta, amsan da Narcissist zai baka idan ka bijiro mishi da wani laifi da yayi to sai ya fi shi laifin bata maka rai saboda Gaslighting da rashin nadama akan laifin. Narcissist ba ya amsa laifin sa (Never takes responsibility), koda kuwa yace maka kayi haquri ya tuba to za ka ga cewa sai ya qara da wasu kalaman da za su nuna cewa ba tuban gaskiya yayi ba ta hanyar ajiye magana, ko saqa magana, ko habaici, ko shagube. Idan ka fahimci cewa mutum Narcissist ne, to kada ma ka yi mishi ‘yar tinqe wato kada ka saka shi a kwana, saboda idan ka sake ka matse shi a kwana, to fa za ka ji babu dadi kuwa. Ya dunga tsilla-tsilla kenan tare da kame-kame wajen ganin cewa ya tsira daga zargi ko ta halin qaqa (Over-rationalization). Domin ya qirqiri qarya kuwa don ya muzanta wani, ko kuma ya wanke kan shi daga wani laifi, wannan mai sauqi ne a wajen shi. Narcissist maqaryaci ne na Allah Ya isa ma, akwai wadanda duk abin da za su fada maka, to sai dai ka ajiye shi a babin qila-wa-qala ma’ana zai iya zama gaskiyane ko qarya ko kuma an hada qarya da gaskiya. Kuma da wuya kaci nasara wajen yin jayayya ko gardama da Narcissist duk kuwa yanda matsalan ta fito fili, idan ya kafe a abu, to da wuya ka iya sauya mishi ra’ayi duk raunin matsayan nasa. Duk Narcissist na aikata Gaslighting amma ba duka mai aikata Gaslighting bane Narcissist, sai a kula. Ko sau 1 mutum ya taba Gaslighting din ka, to ya kamata ka yi hattara da shi, saboda da wuya idan bai cigaba ba.
Sannan kuma Narcissist baya taba canzawa sai dai ya canza daga mummuna zuwa halin da yafi muni. Saboda haka, za ka bata lokacin ka ne kawai wajen qoqarin ganin cewa ka canza shi ko kuma ya karbi laifin shi. Wannan na daya daga cikin jiga-jigan dabi’un Narcissist.
(2) Irresponsibility/Egocentricity/Lack of Empathy
Irresponsibility ta hada da rashin kula da wadanda suke a qarqashin kulawan ka musamman ‘ya’ya da mata ko kuma qin yarda da wani aika-aika da mutum ya tafka. Egocentricity kuma na nufin bala’in son kai (Malicious Self-love), irin son kan da zai jefa mutum ya dunga take hakkin sauran mutane tun ma ba wadanda suka fi kusa a gareshi ba kaman ‘ya’ya da mata. A irin wannan yanayi sai ka samu maigida yana da mata tare da ‘ya’ya amma kuma babu ruwan shi da duk wasu abubuwan da suka shafi iyalin shi kaman ciyarwa, tufatarwa, karatu, da tarbiyya. Sai ya kasance kan shi kadai ya sani, zai fita waje ya ci abinci mai nagarta tare da gina jiki, yaci tsire ya sha shayi amma kuma iyalan sa a kullum da kyar suke ci da sha. Bai damu ya ga cewa ‘ya’yan shi suna yin karatu ba ko kuma bai damu da nagartan karatun ‘ya’yan sa ba. Bai damu da wahalan da matan shi ke shiga ba wajen qoqarin cewa ta ciyar da ‘ya’yan su koda kuwa bata yin aiki. Bai damu da kyawun tufafin da iyalin shi za su sa ba koda kuwa yana da hali.
A irin wannan yanayi, zaka iya samun maigida yana da mota ko kuma ma motocin hawa fiye da daya amma kuma ba zai dunga kai uwargida ko ina a motan shi ba ballantana ya bata nata motan koda kuwa yana yin kyautan motoci ga wasu a waje ga sauran ‘yan’uwan shi da abokan shi. Bayan haka, sai kuma ya kasance yana tauye ma uwargida duk wani hanya da zata samu cigaba a rayuwanta kaman ya hana ta cigaba da karatu ko kuma idan dama tayi karatun, to sai ya hana ta yin aiki ta hanyar fakewa akan dalilin da bai taka kara ya karya ba. Wani har ‘ya’yan da ya haifa zai dunga daqile su ko tadiyar da su a duk lamuran da za su sami cigaba a rayuwan su. Duk da haka, sai kaga cewa wani yana da matuqar kula da wasu mutanen waje wadanda ba su kai kusancin iyalin shi ba. Sai ya iya kashe ma mutane a waje ko nawa ne tare da kula da su amma kuma gidan shi na ci da wuta, wato kaman inuwan giginya kenan, na nesa ka sha, na kusa kuma sai dai ya qonu da rana.
A wasu lokutan, zai iya yiwuwa cewa maigida ba shi da budi sosai, amma kuma duk da haka, da zaran ya samu wasu makafin kudi, a madadin ya inganta rayuwan iyalin sa wadanda suka dade a cikin halin babu, suna malejin rayuwa ne kawai, a’a, sai ka ga kawai ya tafi Qaraye wato ya qara aure. Daga nan kuma sai rashin kulan ya qaru. Wadannan halayyan sune suke nuna tsananin rashin kula (Irresponsibility), tare da bala’in son kai (Egocentricity) har da ma rashin tausayi tare da rashin kara (Lack of empathy). Wadannan dabi’un guda 3, suna jerin sahun gaba wajen gane shin wanda ka ke mu’amala da shi Narcissist ne ko kuwa?
A wani sa’in kuma, yanda wadannan dabi’un guda 3 suke bayyana shine sai kaga maigida yana fifita daya daga cikin ‘ya’yan sa saboda shine dan fari ko kuma yana da sunan baban shi ko maman shi ko kuma wani dalili na daban. Wanda ake fifitawan shine ake kira da Golden Child, ko Crown Prince/Princess, duk abin da yake so za a yi mishi kuma babu wanda ya isa ya taba shi duk laifin da ya yi. Sannan kuma maigida ba ya boye tsananin son da yake yin ma Golden Child din, zai nuna a gaban kowa ta yanda duka sauran ‘ya’yan shi sun sani. Wani lokaci ma idan suna son baban su ya yi musu wani abu to sai sun bi ta hanyar Golden Child sannan za su sami biyan buqata. Matsalan ba anan kadai ya ke tsayawa ba, mafi yawan lokuta sai ka ga cewa daga cikin sauran ‘ya’yan kuma, akwai wanda ake kira Scapegoat Child, wato wanda aka tsana da kuma Invisible Child, wato wanda ba a san ma da shi ba kwata-kwata. Abubuwan da za a dunga yin ma Scapegoat da Invisible Children zai sa su fara ma tunanin cewa ko dai bashi ne baban su ba haka ma sauran mutane za su fahimci irin muzantawan da akeyin musu qarara a fili. A mafi yawan lokuta, sai ka ga cewa dan da aka fi so din (Golden Child) ya zama Narcissist kaman uban shi idan ya girma ya mallaki hankalin shi wato idan ya kai shekara 18 – 25.
Haka zalika, irin wannan fifikon na faruwa a tsakanin mata a inda za ka ga cewa maigida yana fifita daya daga cikin matan sa qarara koda kuwa shi ba Narcissist bane. A mafi yawan lokuta za ka ga cewa wanda ake fifitawan to itace Narcissist din. Yanda abin ke faruwa shine idan akwai Narcissist a cikin matan ka, to za ka ga cewa ta fita daban da sauran matan wajen iya tarairayan ka da tattalin ka da kissa da kisisina da nuna cewa ta fi kowa son ka a duniya tare da kyautata maka ta dukkan hanyoyin zamantakewan aure. To irin wadannan kyawawan dabi’un sai su jawo hankalin maigida a gare ta, amma kash, Narcissists kwararru ne wajen yaudara da hila da mugunta da kisan mummuqe, akwai su da fuska 2. Zuma ne ga zaqi ga harbi! Sai maigida ya sakankance ya bar ma ita Narcissist din wato ‘yar mowa kenan, jan ragaman dukkan harkokin shi na gida, kai har ma da na waje saboda tsaban yarda da yayi da ita. Daga nan kuma sai ‘yar mowa ta fara shuka tsiyatakun ta a hankali wajen yin makirci ga sauran kishiyoyin ta da ‘ya’yan su a wajen maigida. Wannan shine ake kira da Triangulation ko Threesome a karatun Narcissist. Sai ta dunga amfani da maigida ta hanyar kai qaran kishiyoyin ta da ‘ya’yan su wajen maigida domin ya dauki tsatstsauran mataki akan su. Shi kuma maigida, saboda tsabar yarda da yayi da ita ‘yar mowa (Narcissist) sai idon shi ya rufe, ya qi binciken asalin yanda matsalan ya faru kuma ya qi sauraron wadanda aka kawo mishi qaran sai kawai ya zartar da hukunci mai tsauri a kan su. Irin wannan hukuncin zai iya zama fada ne da hantara ko kuma ma saki ko ya kori ‘ya’yan shi daga gidan kwata-kwata. Shawara ga maigida a nan shine kada ka taba sauraron qorafin da daya daga cikin matan ka zata kawo maka a kan kishiyan ta ko dan kishiyan ta. Saboda kishiya dai bata fi kishiya ba, idan har da gaske ne an yi mata ba daidai ba, to ai za ta iya tunkaran ita kishiyan nata domin ta rama ko kuma su warware matsalan ba tare da ka sani ba. Idan kuma dan kishiya ne yayi mata ba daidai ba, to ai itama dan ta ne, saboda haka zata iya tunkaran shi domin tayi masa fada akan abin da yayi mata ba tare da ka sani ba ma. Idan kuma har kana son ka shiga tsakani, to wajibi ne a gare ka da ka yi bincike cikakke tare da jin ta bakin dukkanin wadanda abinda ya shafa kafin ka yanke hukunci. Kada ka yi amfani da cewa ai ka yarda da dukkanin abin da ‘yar mowa za ta fada maka gaskiya ne babu qari akai. Sharrin Narcissist ya wuce haka, sun kware wajen juya labari domin su cimma mummunan burin su wato Manipulation. Alal misali, sai ka ji an kawo maka qaran cewa wai dan kishiyan ta ba ya gaishe ta idan sun hadu. Idan kuma ka bincika sai ka gano cewa yana gaishe ta idan ya ganta amma kuma sai ta qi amsa gaisuwan na shi qiri-qiri wanda hakan ya sa daga baya ya daina gaishe ta. Ko kuma sai ta amsa gaisuwan shi a gaban ka, amma kuma ta share shi a bayan ka. Narcissist mugayen mutane ne, sun san duk hanyar da za su hada husuma ko su tada zaune tsaye. Zai kuma iya yiwuwa cewa shi ma maigidan Narcissist ne kaman ‘yar mowan.
Sai mun hadu a kashi na gaba a inda zan tattake wuri akan Red Flag na 3:
(3) Grandiosity/Entitlement/Showmanship/Carelessness/Greed
Salihu Lukman, Assistant Professor ne na Civil Engineering a University of Hafr Al Batin, Saudi Arabia
Na ilimantu kwarai da gaske na samu sauki akan yaddan zan cigaba da tafyar da rayuwa da irin wadannan mutane da nake mu’amala dasu.jzkl
Madalla, da ma buri na kenan, inga cewa mutane sun fahimci ire-iren wadannan mutanen, amma akwai sauran karatu. Part 3, 4, 5 da 6 suna kan hanya.