Part 4: Narcissist, Zuma Ga Zaqi Ga Harbi, Marmari Daga Nesa

Loading

Part 4: Narcissist, Zuma Ga Zaqi Ga Harbi, Marmari Daga Nesa

Tare Da: Dr. Salihu Lukman

(4) Envy/Jealousy/Histrionic/Controlling /Gossip/Hypocrisy

Narcissist mutum ne mai baqin hassada (Envy) akan duk abu mai kyau da ya same ka. Narcissist ba sa iya boye mummunan hassadan da suke yin maka kuma za su iya aikata komai wajen ganin cewa wannan ni’iman da ka samu ta gushe. Shi kuma a kodayaushe yana zargin cewa sauran mutane suna yin mishi hassada ne a nashi tunanin. Yanda hassadan su ke fitowa fili shine ta hanyar kushe duk wani abu da ka yi sabo sai su nuna cewa ai suna da wanda yafi shi kyau da nagarta ko kuma su nuna cewa ai nasu daga qasan waje ma aka siyo musu bayan kai ba ka tambaye su ba akan ko suna da irin shi. Ko kuma su nuna cewa ai wani dan’uwan su yana da wanda ya fi naka kyau da nagarta. Ba za su taba nuna maka farin cikin su ba a game da wani abu da ka samu sai sun nemi saqa wata maganan da zai bata maka rai. Sannan kuma akwai su da yin tsananin gasa (Competition). Sai ka ga mutum yana bibiyan ka duk wani abun da kayi shima zai ce sai ya yi irin sa, haka nan kuma duk wani abun da siya ko ka mallaka shi ma zai dage yaga cewa ya mallakeshi. Sai ya maida ka kaman wani kishiyan shi, wannan ma nau’i ne na hassada a kula. Yawancin Narcissist ba sa yarda a ci su a Competition, sannan kuma a wajen su, komai abin Competition ne. Duk wanda ka ga cewa baqin hassadan shi a gare ka ta fito fili, to ka kiyaye shi, domin zai iya aikata komai domin ya ga cewa ka durqushe qasa warwas. Iyaye Narcissists haka za ka ga cewa sun sako ‘ya’yan su a gaba, sai su dunga yin ma junan su hassadan duk wani abun alkhairin da ‘ya’yan na su za su yi musu. Uba ya ji haushin cewa dan shi yayi ma maman shi kyauta, ko kuma uwa ta ji haushin cewa dan ta yayi ma baban shi kyauta. Idan kuma daya ne daga cikin iyayen Narcissist kaman ace uba, to sai kaga ya sa ma ‘ya’yan na shi ido akan duk wani kyauta da za su ba uwan su, idan suka sake ba su yi mai irin wannan kyautan ba, to babu kwanciyan hankali a gidan duk da fifikon uwa akan uba da musulunci ya tabbatar. Narcissist akwai sa ido ga tsananin kwadayi da rashin dattaku.

Bayan hassada, sai kuma bala’in kishi wanda ya wuce na al’ada da Sharia. Idan mijin ne Narcissist, zai kasance a kullum yana bibiyan wayanta, saqonninta, da tattaunawan ta (Chats) ko da kuwa babu wani buqatan yin hakan. A wani lokacin ma sai ya hana ta amfani da wayan kwata-kwata ko ya kwace, ko ya dunga zargin ta akan abubuwan da bata ji ba bata gani ba. Har ta kai ga ya hana ‘yan’uwan ta kawo mata ziyara ko kuma ma yayi mata kulle gabaki daya (Coercive Control) ta hanyan hana ta zuwa ko’ina koda kuwa wajen iyayen ta ne ko zuwa wani sha’anin ‘yan’uwan ta.

Idan kuma matan ce Narcissist din, to sai ka ga cewa tana kishi da duk wata da ta rabe shi ko da kuwa maman shi ne. Idan kuma akayi rashin sa’an cewa tana da kishiya ko kishiyoyi, to fa maigidan ya shiga 3 a hannun ta domin a kullum sai an yi mai qorafi kala-kala. Idan ya biye ma qorafe-qorafen ta wadanda ba za su taba qarewa ba, to sai ya ji kaman kan shi zai buga. A irin wannan yanayin, bala’in da za ta dunga yin mai luguden su akai-akai zai iya sabbaba ma maigida matsalolin da suka shafi Mental Health kaman Depression (na yi cikakken bayanin shi a maqala ta a baya), ko kuma Physical Health din shi ya tabarbare. Yin kishiya da Narcissist ba qaramin annoba bane saboda girman kaidin su ya baci. Ba dole ta dunga tunkaran kishiyan ta da husuma ba, saboda basa son abin da zai kunyata su a gaban jama’a, sun fin son su yi kisan mummuqe ta hanyar mallake mijin da hila da kissa da kisisina daga nan kuma sai su yi amfani da shi wajen diramma kishiyan su wato Triangulation. Sai ka ji mutane suna cewa ai ta yi mai asiri ne shiyasa ta mallake shi bayan babu wani asirin da ta yi mishi, zabagen hila ce da tsananin wayo irin na Narcissist. A wani lokacin fa, har yin qaryan ciwo za ta iya yi domin kawai hankalin mijin ya dawo kanta. Za ta iya yin qaryan ciwon aljanu, ko hauka. Akwai wanda na sani ta ke yin qaryan ciwon hauka domin a kwantar da ita a Psychiatric Hospital kawai saboda hankalin mijin ya dawo kanta sannan kuma iyayen shi su yi jinyarta. Wata kuma zata yi amfani ne da rashin lafiyan dan ta ta dunga daga hankalin mijin a duk lokacin da yake da kwana a gidan kishiyan ta. Wata za ta iya neman kashe kanta ta hanyar amfani da reza domin ta yanke jijiyan hannun ta kawai don jan hankalin mijin ta. Akwai wanda na sani cewa ta yi qaryan suma a cikin gidanta alhali kuma mijin ta yana wani gari daban. Nan take, ya yi hanzarin tura abokin shi tare da motan daukan mara lafiya na gaggawa na asibiti wato Ambulance. Su ka isa gidan domin su dauke ta zuwa asibiti don a duba ta, ashe suman qarya ta yi domin ta janyo hankalin mijin nata ya dawo daga tafiyan da yayi. Da ya qi dawowa, sai ta qara shirya wani sabon qaryan ta ce mai anayin mata qarin jini tare da bata iskar Oxygen ta hanci a asibiti saboda rashin lafiya, ai daga jin haka, sai yayi hanzari ya dawo wajen ta babu shiri saboda gudun faruwan mummunan abu, ya bar sabon auren shi da yayi na sati 2 kacal, an katse ma bawan Allah Honeymoon din shi. Har ila yau, akwai kuma wata da dan ta ya kamu da ciwo da tsakan dare bayan mijin ta yayi bacci kuma yana gidan kishiyan ta ne amma ciwon bai kai ace za’a je asibiti ba, sai kawai ta sa aka taso shi da sunan wai zata kai yaron asibiti a duba shi da tsakan daren domin kawai ta ja hankalin mijin su tafi asibiitin da daddaren. Bayan da mijin ya je ya ga mara lafiya kuma ya sami natsuwan cewa ciwon ba na tafiya asibiti bane a cikin gaggawa, sai ya kyale matan na shi ta kai dan asibiti ita kadai, ya nuna cewa shi ba zai je ba. Har matan ta goya dan, ta fito da motan ta daga Gate din gidan, da taga cewa mijin ya qi ya bita yana da niyyan komawa baccin shi, sai kawai ta tuqo motan ta shigo da shi cikin gidan ta kulle Gate din ta koma ta shige gidanta. Wannan mijin ya tsallake tarkon da ta dana mishi. Wata matan fa duk sanda ta ga cewa mijin ta na cikin walwala da farin ciki tare da daya daga cikin kishiyoyin ta, to fa sai ta qirqiro wani abun daban wanda zata dagula wannan zaman lafiyan da ya samu. Ire-iren wadannan misalan suna da dumbin yawa.

Idan ta yi sa’an miji talasuru, to sai kaga cewa ta sami yanda take so, sai tayi ta cin karanta babu babbaka. Ko da ace ta sami tsayayyen namiji, to zata iya cin karen ta babu babbaka har zuwa lokacin da zai gano cewa juya shi kawai take yi tamkar sitiyarin mota, to fa daga nan kuma, labari zai sauya, domin za ta tashi daga ‘yar mowa zuwa ‘yar bora idan ma bai rabu da ita ba kenan kwata-kwata saboda illan da ta yi mishi a rayuwan shi da na sauran iyalin shi. Dole mu guje ma auren Narcissist, idan ba haka ba kuma to matsalolin mu na aure sai dai su yi ta qaruwa kaman duhun dare. Babban hanyan da za mu guje musu shine mu fahimci halayyan su sosai ta yanda zamu iya gane su a lokacin neman aure wato Courtship. Da zaran kuwa mun gano su, to sai mu dafa qeya mu ranta a na kare muce qafa me naci ban ba ka ba. Saboda da mugun rawa gara da qin tashi. Auren Narcissist na daya daga cikin bala’o’in duniya. Saboda idan suka yi maka wani illa a zuciyar ka, to fa har ka koma zuwa ga mahaliccin ka zuciyar ka za tayi ta zubar da jini, ba a samun waraka daga cutarwan su sai dai ayi rigakafi tafi magani wato a guje musu kwata-kwata idan ba haka ba kuwa, to jiki magayi.

Irin wadannan hanyoyin da Narcissists ke bi domin janyo hankalin mazajen su ko daga musu hankali saboda kishi ko wani abun daban suna da yawa sosai kuma ana siffanta su da Histrionic wato kaman ‘yan dirama su ke ji. Kuma maza ma suna da hanyoyin da suke yin na su diraman, kaman yanda za ku ga wadanda aka gurfanar a kotu domin wawushe kudin al’umma ko wasu laifuffukan kwatsam sun bayyana a kan keken guragu, ko gadon asibiti mai taya tare da bandeji ya lullube su, ko yin suman qarya a yayin da akeyin musu da aka turke su wajen yin tambayoyin qeqe-da-qeqe. Wani ma a 2018 durowa yayi daga motan Police a tsakiyan titi ya fara wasu ayyayyakai a yayin da za su kai shi kotu. Akwai Mental Disorder mai zaman kanshi mai suna Histrionic Personality Disorder (HPD) wanda ya qunshi ire-iren wadannan dabi’un na neman jan hankalin wani ko ta halin qaqa ko kuma qoqarin cinye taro ta hanyar magana ko shiga mai jan hankali (Sexually Seductive or Provocative Behavior) domin ya kasance hankalin kowa na kan mutum, ko dora hotuna ko bidiyo masu jan hankali da daga sha’awa a Social Media da dai sauran halayyan rashin kamun kai. Bayan nazarin HPD mai zurfi da Psychiatrists suka yi, sun gano cewa kusan dukkanin masu dauke da HPD to za ka ga cewa ko dai suna dauke da Narcissistic Personality Disorder wato Narcissists ne ko Borderline Personality Disorder (BPD, nayi bayani a kan shi a cikin maqala ta a baya) sannan kuma alamomin HPD suna dunqule a cikin rarrabuwan kashe-kashen NPD da BPD. Saboda haka, suna ganin cewa HPD bai kamata ace ya zauna a matsayin wani kashi na daban mai cin gashin kan shi daga cikin Mental Disorders ba tun da NPD da BPD sun laqume shi. Ina so mu sani kuma cewa NPD da BPD ba sa taba haduwa a mutum guda, ma’ana, mai dauke da BPD ba zai yiwu kuma ace ya zama Narcissist ba haka kuma wanda yake Narcissist ne ba zai yiwu ace yana dauke da BPD ba duk da yake suna gida daya ne wato Cluster B Personality Disorders (NPD, HPD, BPD, ASPD) amma kuma kowa da dakin shi. Duk da yake NPD da BPD ba sa haduwa, amma kuma yanayin dabi’un masu dauke da su, suna yin kama da juna sosai a lokuta da dama har ma ta kai ga cewa za ka iya yin kuskuren siffanta mutum da BPD bayan a haqiqanin gaskiya Narcissist ne. Shi yasa Dr. Ramani ta ke cewa idan aka hada Narcissist da mai BPD a daki guda, to ka yi marmaza ka fice daga dakin saboda irin hatsaniyan da zai iya faruwa ya wuce tunanin ka. Narcissist ga fushi ga naci ga tsokanan fada ga rainin hankali da gasa magana, shi kuma BPD ga shi abu kadan zai iya tunzura shi ya fusata, ga shi ba a ce mai kule sai ya amsa da ca-cas-cas kuma baya daukan rainin wayo kuma ko da ace abu ya huce har ya sallace to fa sai ya maida martani ga bala’in fushi mai tuqa (Rumination) da daukan fansa. Babban bambanci tsakanin BPD da NPD shine yanda kowannen su yake daukan kan shi wato Self-Image ko Sense of Self. Mai BPD yana da rashin tabbatuwa a abin da ya saka a gaba ko ya qudurce a ran shi (Unstable Self-image or Identity Disturbance). A irin wannan yanayin, mutum sai ya kasance ba shi da tabbatuwa a abin da yake so ya cimma buri a rayuwarsa, sai ya dunga saurin cancanza aikin da ya ke son yi, ko ra’ayin shi akan abubuwan da ya tabbatu akai a baya. Wani zai iya canza abokan shi, ko kuma ma jinsin shi gabadaya ko yin ridda ko kuma ya ce babu Allah gabadaya (Atheist) ko kuma ya samu shakka kan akwai Allah ko kuwa babu shi (Agnostic) bayan a baya ya yi imani da Allah sosai kuma mai bin addini ne. Duk da haka, mai BPD yana iya samun damuwa daga wadannan alamomin da suke addaban shi kuma suke addaban harkokin shi na yau da kullum, saboda haka mai BPD zai iya kasancewa Egodystonic kenan. Har ma idan ya fahimci abin da ke damun shi wato ya samu cikakkiyar Insight har ya iya zuwa wajen Mental Health Professionals domin neman lafiya, kuma zai iya samun sauqi ta hanyar Psychotherapy mai suna DBT (Dialectical Behavior Therapy). Shi kuma Narcissist, ya yi imanin cewa ya fi kowa ga tsananin jin kai (Grandiose, Inflated Sense of Self-importance) amma kuma duk da haka ba shi da natsuwa akan kan shi (Insecure Self-image), a kodayaushe yana neman ana yaba mishi (Seeking Validation and Admiration) kuma yana tsananin tunani akan yanda ake daukan shi (Fragile Self-esteem). Sannan kuma bugu da qari, baya jin wani damuwa a game da dabi’un shi ko kuma dangane da yanda yake mu’amala da mutane, wato shi Egosyntonic ne kishiyan mai BPD. Narcissist ba ya samun warakan da zai iya rayuwa ba tare daya cusguna ma abokin mu’amalan shi ba koda kuwa yana ganin Mental Health Professional. A taqaicen taqaitawa dai shi Narcissist baya canzawa kuma ba ya warkewa. Sai dai ka fahimci yanda za ka iya zaqulo shi daga cikin al’umma domin kwararre ne wajen iya sajewa da mutanen kirki da boye muguntan sa. Idan ka gano shi kuma, daga nan sai ka bi hanyoyin da ya kamata wajen yin mu’amala da shi idan har ya kasance dole ne sai ka yi mu’amalan da shi. Zan yi qarin bayani a game da wadannan hanyoyin a Part 6 na wannan jerangiyar maqalolin a kan Narcissist. Ka sani cewa guje mishi shi yafi alhairi idan hakan zai yiwu. To me kuma za ku iya cewa idan aka samu mai dauke da BPD ya auri Narcissist? Husuma a gidan ba zai taba yankewa ba kenan, ya samu wajen zama na dindindin idan ba su rabu ba kenan.

Narcissist ba ya son kadaici ko kadan saboda yana da buqatan ace akwai wani a gefen wanda zai dunga yaba mishi ko tabbatar da shi akan abin da yake yi (Needs Constant Admiration and Validation). A saboda haka, baya son zama shi kadai. Ko dai ya yi ta gayyato mutane gidan shi da sunan hira ko ziyara ko liyafa, ko kuma ya dunga fita waje domin bibiyan duk inda zai hadu da jama’a kaman wajen buki ne ko kuwa taro ko wani sha’anin daban. Zuwan Social Media sai ya sauwaqe mishi buqatan sai ya fita waje, domin zai zauna a wuri guda amma sai ka ji duk daqiqa daya sai wayan shi ta yi qaran shigowan saqo daga Text ne, ko kuwa hiran WhatsApp Group ne ko dai sauran saqonnin daga Facebook ko Twitter ko TikTok ko Instagram. Wannan ya shafi masu neman jan hankalin mutane a Social Media ta hanyanyoyin da suke nuni ga rashin kamun kai kaman raye-raye, ko kalaman batsa tare da shiga masu daga sha’awa (Seduction) saboda neman shuhura tare da samun Likes da Followers da Views. Kuma ba sa son a kushe su komin qanqantan kushewan kuwa, yanzu hankalin su zai tashi ko kuma ma su maida martanin da yafi kushewan da akayi musu. Har da masu tallata rayuwan su kacokan a Social Media, yau sun sa wancan kayan, gobe sun tafi wancan qasan, gata kuma sun tafi yawon shaqatawa. Lalacewan ta kan kai ga wasu suna da aure amma kuma sai su dunga yin mu’amalan cin amanan iyaln su wanda bai dace ba (Emotional Infidelity and Microcheating) da mata ko mazan da ba na su ne ba a Social Media ko kuma a wajen Social Media har ma ta iya kaiwa ga zina ko kuma zinace-zinace (Sexual Infidelity).

Wani lokacin kuma, sai ya wuni akan waya yana ta hira domin ya rage mai kadaici sannan kuma ya sami bayanai wadanda suka shafi sauran mutane. A irin wadannan hira-hiran ne marasa ma’ana, sai ka ga cewa gulma (Gossip) ta shigo ciki ta yi kane-kane. Sai ya dauki labarin wannan, ya juya shi yanda ya ke so, ya iyar ma wani daban ko da kuwa isar da labarin zai iya haddasa husuma ko gaba ko rashin jituwa a tsakanin mutanen. Kunga anan, ya zama munafiki kuma algungumi. Dama can, Narcissist kwararre ne a wajen yin fuska biyu. Zai iya ma haba-haba ya nuna cewa yana tare da kai da abun da ka ke kai dari bisa dari amma kana juya baya sai ya fara zagin ka a gaban wasu ko kuma ya kwashe sirrin da baka son kowa ya sani ya yada ma wasu don ya bata ka (Hypocrisy). Dole maza su kiyaye wadanda matan su ke hulda da su, saboda mata sun fi kwarewa a wajen algungumanci tun ba wadanda suke zaune basa zuwa aiki ba sai dai kullum ana yawon kai ziyara ko hira a makwabta. Ko da kuwa suna zuwa wajen aiki, to za ka ga cewa sai su sami inda za su dunga haduwa ana yin hira, a makaranta ne ko kuwa a asibiti. Duk sanda ka gano wata algunguma daga cikin qawayen ta, to dole ne ka raba ta da ita ta kowane hanya, idan ba haka ba kuwa, kana zaune zaka ga BBC ko CNN suna bayani akan abubuwan da suke faruwa a cikin gidan ka, ko kuma ta hada ka husuma da matan ka ko kuma ta yi ma matan ka sharri da qazafin da bata jiba bata gani ba.

Akwai wata da tayi qawance da Narcissist, har ta kai ga cewa tana bata masauki ta kwana a gidanta idan ta shigo gari. Kwatsam sai suka hadu a wani gida sun je yin gaisuwar mutuwa. Narcissist din ne ta shigo inda take ta zauna. Suna cikin zaman karban gaisuwa, kawai sai Narcissist din ta ce wai ita qawar ta sace mata waya bayan kuma bata shigo da wani waya ba. Daga qarshe dai har sai da ita qawan ta maka Narcissist din a kotu saboda qazafin da ta yi mata. Don Allah ku gani, qawar ta ce fa amma ta rasa sharrin da za ta yi mata sai na sata. Ku gane cewa Narcissist ya fi illan ta wanda ya fi kusa da shi kaman iyalin shi ko abokan shi ko wadanda suke qarqashin shi a matsayin ma’aikata da sauran wadanda suke yin mu’amala ta qut-da-qut. Haka nan akwai wata algunguman ita ma da ta surfafi iyalan wani, ta dunga yawo da bayanan matan shi a tsakanin su, sai ta dauko sirrin wannan matan, sai ta dire shi a wajen dayan matan, kuma tana canza bayanan da qarin gishiri domin ta tunzura su. Cikin ikon Allah, sai mijin ya gano ta, ai tuni yayi ma matan shi gabadayan su haramcin yin mu’amala da ita kwata-kwata. Narcissist ba qananan algungumai bane, a yi hattara. Za su iya kashe aure, kuma za su iya lalata auren ma tun kafin a yi shi. Bincike mai zurfi da sa ido akan abubuwan da ke faruwa na daga cikin abubuwan da suke warware illololin da Narcissist suke qullawa. Kada ka taba yaudaruwa da siffan mutum, ko riqon shi da addini, ko iya bayanin shi, domin Narcissists kwararrune wajen iya yaudara da ha’inci da juya mutum yanda suke so (Manipulation) da yin amfani da laggon ka wajen biyan buqatan su wato Exploitation. Akwai su da wayau, ga rashin wayau, ga rainin wayau, duk sun hade musu.

Sai mun hadu a kashi na gaba a inda zan tattake wuri akan Red Flag na 5:

(5) Aggressive/Sadist/Baiter/Hypersensitive/Paranoid

Salihu Lukman, Assistant Professor ne na Civil Engineering a University of Hafr Al Batin, Saudi Arabia



Tagged : / / / / / / / /

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *